
Daga BELLO A. BABAJI
Aƙalla fursunoni 6,675 da suka haɗa da manyan ƴan Boko Haram da makasa suka tsere a gidajen yari mabanbanta 13 cikin shekaru biyar a Nijeriya.
Rahotonni sun bayyana cewa, kaso 30.4 ne jami’ai suka yi nasarar sake kamowa yayin da aka rasa kama 60.5.
Na kwanan nan shi ne wanda ya auku a ranar Talata a jihar Borno, sakamakon ambaliyar Maiduguri inda fursunoni 289 suka tsere bayan rushewar wani ɓangare na ginin gidan yarin birnin.
Wani jami’i da aka zanta da shi game da lamarin, ya tabbatar da cewa, wasu kwamandodin Boko Haram da ke tsare a gidan sun samu tserewa.
Haka nan, wani da bai bayyana sunansa ba ya ce lamarin ya auku ne a lokacin da ake tsaka da gyaran gidan yarin wanda aka gidan shi tsawon shekaru 30 da suka gabata.
A lokacin da ya ke tsokaci game da batun, Ministan Ma’aikatar Harkokin Cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ya tabbatar da cewa ambaliyar ta shafi wasu sashi-sashi na gidan yarin yayin da ya ce su na cigaba da bincike game lamarin.
Haka nan, kakakin Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali, Umar Abubakar ya tabbatar wa al’umma cewa hukumarsu tare da sauran hukumomi na aiki tuƙuru wajen ganin an samar da tsaro a cikin su.
