Edo 2024: Shettima da Ganduje sun shiga sahun masu nema wa Okpebhol ƙuri’a

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya roƙi al’ummar Jihar Edo su zaɓi ɗan takarar APC, Sanata Monday Okpebhol a zaɓen gwamna da za a yi a ranar Asabar don samun shugabanci mai inganci.

Shettima, wanda ya halarci taron rufe yawon neman zaɓen ɗan takarar tare da wasu jiga-jigan jam’iyyar a Benin babban birnin jihar, ya ce a halin da ake ciki, Edo ta na buƙatar jagora mai basira da iya gina al’umma wanda zai kai ga samun nasarori ga mutanensa.

Ya kuma bayyana wa al’ummar jihar cewa, samun jiha mai cike da damanmaki shi ne burinsu don haka al’umma su yi watsi da batutuwan bambance-bambance da ke tsakaninsu wajen zaɓar ɗan takarar don cimma hakan.

Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma yi tsokaci game da ci gaba da aka samu a ɓangaren samun kuɗin shiga ga dukkan ɓangarorin gwamnati, ya na mai kira a gare su da yi wa APC ruwan ƙuri’u don samun damar amfana daga sauyin ci gaban da aka samu.

Kazalika, Shettima ya tabbatar da cewa, gwamnatin Shugaba Tinubu na cigaba da ƙoƙarin kai ƙarin kayayyakin tallafi ga waɗanda ambaliyar ruwan sama ta rutsa da su a sassan Nijeriya.

Sauran mahlarta taron sun haɗa da; Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje; tsohon shugaban jam’iyyar kuma tsohon gwamnan jihar, Adams Oshiomhole; Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio da sauran su.

By Babaji