Aƙalla mutane 40 sun halaka a hatsarin jirgin ruwa a Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Aƙalla sama da mutane 40 ne suka mutu da suka haɗa maza da mata a kogin Gummi da ke ƙaramar hukumar Gummi ta jihar Zamfara.

Daraktan Hukumar bada Agajin Gaggawa ta jihar (ZEMA), Hon. Hassan Dauran, ya shaida wa manema labarai cewa, jirgin na ɗauke ne da fasinjoji sama da 50 a lokacin da hatsarin ya auku.

“Kamar yadda na ke magana a yanzu, kaɗan ne daga cikin su aka ceto da ransu a lokacin, yayin da mafi yawan fasinjojin, galibi mata da ƙananan yara sun hallaka.”

A zantawarsa da wakilinmu ta wayar tarho, wani direban ɗaya daga cikin waɗanda suka tsira da ransa mai suna Malam Yunusa ya ce, fasinjoji goma sha biyu ne kawai aka ceto yayin da lamarin ya faru.

Ya ce, ya garzaya don ceto fasinjojin, kuma a cikin haka ne kwale-kwalen nasa ya samu matsala a cikin kogin wanda nan take shima ya kife.

“Nan da nan muka fahimci cewa kwale-kwalen da ke jigilar fasinjojin na shirin nutsewa a cikin kogin sakamakon yawan lodin da ya yi, na ɗauki nawa kwalekwalen domin ceto fasinjojin amma abin takaici kwale-kwale na ya samu matsala kuma ya kife, inda muka samu nasarar ceto goma sha biyu daga cikinsu yayin da fiye da mutum arba’in an nutsar da su cikin kogin nan take,” inji Malam Yunusa

Mai Martaba Sarkin Gummi, Mai Shari’a Hassan Lawal (mai ritaya), ya jajenta wa iyalan waɗanda suka rasa rayukan nasu a lamarin.

Ya kuma bayyana lamarin a matsayin abin tausayi tare da yi musu addu’ar Allah ya gafarta wa duk waɗanda suka rasa rayukansu, ya kuma bai wa iyalansu haƙurin jure rashin.

A nasa ɓangaren, shugaban ƙaramar hukumar Gummi, Hon. Na’Allah Musa, ya alaƙanta lamarin da sanya mutane fiye da kima a jirgin.

“Matakin jirgin ya buƙaci wasu fasinjojin kafin su tashi su sauka saboda rashin tsaro, amma suka ƙi, kuma lodin da aka yi shi ne babban sabanin da ya haddasa lamarin.”

Hon. Musa ya buƙaci matafiya da shugabannin kwale-kwalen da ke yankin da su guji yin lodin da ya wuce kima a lokacin da su ke tafiya a kan kogin domin gudun sake aukuwar irin lamarin a nan gaba.

By Babaji