A wani cigaba da aka ƙara samu a yaƙi da ƴan ta’adda a yankin Arewa a Nijeriya, jami’an tsaro sun yi nasarar kashe wani babban ɗan ta’adda mai suna Sani Wala Burki wanda ya shahara a yankin Safana da Batsari.
An samu nasarar kashe Sani Wala ne a wani sumame na haɗin gwiwa da jamian tsaro da kuma yan sanda sa kai na Jihar Katsina. Harin ya biyo bayan bayanan sirri da jami’an tsaro su ka samu na cewa Sani da tawagar sa na shirin kai hari a wani yanki na Safana.
Samun nasarar kashe Sani Wala ba ƙaramin lamari ba ne domin ya kasance shine jagora a wannan yankin, kuma rashin sa zai kawo babban cikasa ga ayyukan ta’addanci a wannan yankin.
Kashe shi ya biyo bayan samun nasarar da jami’an tsaro su kai a kan wani babban ɗan ta’adda Sububu a yankin Maru da ke Jihar Zamfara.
