A yammacin Lahadi da ta gabata ne, tsohon shugaban ƙasa Obasanjo ya isa birnin Minna domin ganawa da tsohon shugaban ƙasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida a gidan sa da ke minna. Wannan ya faru ne jim kaɗan bayan Obasanjo ya halarci bikin cika shekaru 90 na Gabriel Igbinedion a jihar Edo.
Taron a minna basu kaɗai ba ne domin har da tsohon shugaban ƙasa Janar Abdulsalami Abubakar da tsohon mai ba shugaban ƙasa shawara ta fannin tsaro, Janar Aliyu Gusau.
Har yanzu dai ba a san takamaimai abinda suka tattauna ba sai dai rahotanni na nuni da cewa tsofaffin shugabannin ƙasar sun tattauna ne a kan yanayin ƙasa da halin matsin tattalin arziki da ƙasar ke fuskanta.
Sai dai mai taimakawa Obasanjo kan harkokin yaɗa labarai ya bayyana cewa Obasanjo ya kai ziyarar ne domin taya shi IBB murnar cika shekaru 83 domin bai samu damar halartar taron bikin ba lokaci da ya gudana.
