
Daga BELLO A. BABAJI
Rundunar sojin Nijeriya ta tabbatar da kashe shahararren ɗan ta’adda, Ɓaleri Fakai a Zamfara wanda na hannun dama ne ga sanannen shugabansu, Bello Turji.
Ɓaleri na ɗaya daga cikin ƴan ta’adda 30 da jami’an suka halaka a wani artabu da ya auku a tsakanin su a ƙaramar hukumar Maru ta jihar.
Rahotonni sun bayyana cewa, Fakai na ɗaya daga cikin ƴan bindigar da suka addabi yankin Arewa-maso-Yammacin Nijeriya wanda gabannin kashe shi, sai da ya yi iƙirarin ya gagara kamar yadda aka gani a wani faifan bidiyo.
Rahotonnin sun kuma tabbatar da cewa jami’an sojoji sun yi nasarar kashe shi ciki har da rubutun da tsohon mai taimaka wa tsohon shugaban ƙasa kan kafar sada zumunta, Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na X.
Fakai na ɗaya daga cikin manya kuma sanannun ƴan bindiga da aka kashe a ƴan kwanakin nan. Sauran sun haɗa da Ibrahim Nagure, Lawali Dodo, Ƙadiri da Jambaleri a atisaye mabanbanta a Zamfara.
