‘Yan bindiga sun tare hanyar Tsafe-Funtua, sun kashe fasinjoji da dama

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Rahotanni da dama sun bayyana cewa, wasu ɗimbin ƴan bindiga sun tare babbar hanyar da ta haɗe ƙananan hukumomin Tsafe da Funtua a yankin Kucheri tare da kashe mutane da dama.

Wani shaida ya ce, ƴan bindigar su zo ne ɗauke da wasu muggan makamai inda suka yi ta buɗewa mutane da motoci wuta.

Jaridar ‘Spectacules’ ta zanta da Hakimin yankin ta wayar tarho wanda ya ce mutane da dama sun rasa rayukansu a yayin harin inda a halin yanzu hukumomi na gudanar da bincike game da lamarin don samun cikakken bayani.

Sauran bayanai za su fito daga baya yayin da hukumomi ke ƙoƙarin bai wa waɗanda lamarin ya shafa kulawa.

By Babaji