Majalisar Wakilai da Sojoji sun fara binciken zargin tsare jami’i Abbas ba bisa ƙa’ida ba

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Christopher Musa ya umarci a gudanar da bincike game da tsare wani jami’in sojan ruwa mai suna Abbas Haruna da aka ce an yi ba bisa ka’ida ba.

Cikin wani shiri na Brekete Family da aka yi, an ga inda matar sojan ta ke bayani wadda ta ce an tsare shi har na tsawon shekaru shida.

Cikin wata takarda da Daraktan Labarai na sojoji, Janar Tukur Gusau ya fitar, Janar Musa ya ce a gaggauta gudanar da bincike kan lamarin.

Haka ma, cikin wata takarda daga ɗan majalisar wakilai Yusuf Gagdi wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar kan harkokin sojojin ruwa, ya bayyana tsare sojan a matsayin rashin imani.

Gagdi ya ce, kwamitinsa zai yi bincike kan lamarin tare da tabbatar da cewa an hukunta duk waɗanda ke hannu acikin laifin kamar yadda doka ta tanadar.

By Babaji