Mutum 13 sun mutu yayin da 108 ke karɓar kulawa sakamakon ɓarkewar kwalara a Jigawa

Spread the love

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse

Kimanin mutane 13 ne suka mutu acikin wata guda sakamakon ɓarkewar cutar amai da gudawa da aka fi sani da kwalara a ƙaramar hukumar Auyo da ke Jihar Jigawa.

Jami’in Kiwon lafiya a matakin Farko Na ƙaramar hukumar, Malam Abdullahi Musa Auyo ya tabbatar da faruwar lamarin.

Musa Auyo ya shaida wa wakilinmu haka a lokacin da hukumomin RUWASA da na bada agajin gaggawa ta UNICEF suka ziyarci ƙaramar hukumar don bada kayan agaji ga marasa lafiyar tare da ɗaukar matakan kariya don hana cigaba da yaɗuwar cutar a yankin.

Ya ce, an samu ɓarkewar cutar ne a ƙauyuka 12 da ke ƙaramar hukumar ta Auyo waɗanda suka haɗa da; Gatafa,Tsaka, Tsidir, Unguwar Laberiya ke garin Auyo da Ayama, Bayi, da Marau, Akubushi, Kalagwai da sauransu.

Ya ƙara da cewa, cutar ta samu yaɗuwa ne sakamakon anfani da gurɓataccen ruwan sha wanda ya lalata musu rijiyoyin sakamakon yaɗuwar ƙazanta da ta gurɓata ruwan da su ke anfani dashi ta hanyar yin ababe da dama.

Ya kuma ce, a kalla mutane 108 ne aka kwantar daga wata ɗaya zuwa lokacin da ya ke zantawa da wakilin namu sakamakon kamuwa da cutar ta kwalara wadda ake ba su magani a manya da ƙananan asibitocin yankin yayin da wasu da dama aka kwantar dasu a babban asibitin kwanciya da ke Hadejia (Hadejia General Hospital) yayin da aka kwantar da wasu a mabanbanta asibitocin ƙaramar hukumar don ceto rayukansu.

Sakamakon haka, ya sa ƙaramar hukumar ta samar da magunguna na kimanin Naira miliyan biyar a kyauta don rabawa ga ɗaukacin manya da ƙananan asibitocin yankin da nufin yaƙar cutar don ganin an kawo ƙarshen ta Cikin sauki

Kazalika, ya ce ƙaramar hukumar ta gyara ɗaukacin Rijiyoyin tuka-tuka da suka gurɓata sakamakon ambaliyar ruwa sama.

Da ya ke ƙarin haske akan matsalar yaɗuwar cutar, Malam Zulkalraini Gatafa, mazaunin Unguwar Madaki a ƙauyen Gatafa, ya ce lamarin ya wuce duk yadda jama’a suke faɗa, ya na mai cewa sama da mutane talatin ne suka mutu a ƙauyensu kaɗai, amma ba mutane 13 ba kamar yadda wancan jami’in kiwon lafiya matakin farko ya faɗa.

By Babaji