Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
A ranar Talata ne ‘yan bindiga suka taru a gidan Marigayi Kachalla Halilu Sububu da ke Tungar Daji, Bagega, cikin ƙaramar Hukumar Anka ta Jihar Zamfara, domin zaɓen sabbin shugabanni.
Idan dai ba a manta ba jami’an tsaro sun yi nasarar kashe Kachalla Halilu da wasu ‘yan ƙungiyar sa kwanan nan.
Wani mai sharhi kan harkokin tsaro a Sakkwato, Bashiru Altine Guyawa, ya kuma bayyana cewa ‘yan ta’addan za su fara da addu’ar kwana uku ga Marigayi Kachalla Halilu Sububu, sannan a zaɓi sabon shugaba da zai maye gurbinsa.
A yanzu haka suna baje kolin kuɗin da Kachalla Halilu ya bari a gidansa, saboda wasu kuɗaɗe sun lalace yayin da wasu kuma suka ruɓe bayan an daɗe ana ajiye da su.
A cewarsa, ‘yan fashin sun buɗe buhu sama da ɗari biyu cike da kuɗi, sannan kuma suna fitar da zinare da sauran duwatsu masu daraja da Marigayi Sububu ya ɓoye a gidansa domin rabawa.
