
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmummuni Kabir Usman ya naɗa mataimakin gwamnan Jihar Katsina, Farouk Lawal Joɓe a matsayin Sarkin Fulanin Joɓe.
Shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar, Alhaji Jabiru Salisu Tsauri shi aka bai wa matsayin lamiɗon Katsina.
Akwai kuma shugaban kwamitin harkokin cikin gida na majalisar wakilai da ke wakiltar mazabar Matazu da Musawa, Alhaji Abdullahi Aliyu a matsayin Dujuman Katsina.
A jawabinsa bayan naɗin nasu, Sarkin ya nuna jin-daɗinsa ganin yadda manyan jami’an gwamnati ke nuna sha’awarsu ta shiga harkar Masarautar Katsina da Daura.
Ya ce, babu shakka haka zai kawo karin fahimta da haɗa karfi da karfe wajen ci gaban jihar.
Haka kuma ya jaddada cikakken goyon bayan Masarautar ga gwamnatin Dikko Raɗɗa da cigaba da bada haɗin-kai ga gwamna wajan ƙoƙarin na ciyar da jihar gaba .
Sarkin ya kuma nuna takaicinsa kan yadda bala’o’i suka yawaita a jihar inda da ya ce babu wata mafita illa a koma ga Allah.
“Ɓarnan ambaliyar ruwa, satan mutane da amsar ƙudin fansa, ta’addanci da mu’amulla da miyagun ƙwayoyi sun yawaita a jihar. Ba mu da wata mafita sai mu koma ga Allah”, inji Sarkin.
Gwamnan jihar Katsina malam Dikko Radda wanda shima ke riƙe da sarautan Gwagwaran ɗin Katsina tare da ƴan majalisar zartarwa na jihar sun halarci bikin naɗin.
Akwai kuma mataimakan gwamnnonin jihpo Kano da Zamfara, waɗanda su ma suna halarci bikin.
Sai tsohon gwamnan jihar, Aminu Bello Masari da ƴan majalisar dokoki na ƙasa da na jiha waɗanda da su ma suka shaida bikin naɗin sarautun.
