
Daga BELLO A. BABAJI
Tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Zamfara kuma mai taimaka wa tsohon gwamna Bello Matawalle na musamman, Sani Shinkafi ya gargaɗi gwamna mai ci a yanzu na jihar, Dauda Lawal ya ƙaurace wa yaɗa zargin ƙarya akan takwarorinsa na siyasa a jihar.
Ya ce, wasu daga cikin ayyukan gwamnan sun nuna kamar bai san doka ba kuma ya na shakkar bayanan matsayin ƙaramin Ministan Tsaro, Dakta Bello Matawalle.
Shinkafi ya buƙaci gwamnan ya fito ya bayyana matsayarsa game da wani jawabi da aka ce ya bazu a kafafen sadarwa da ke nuna cewa gwamnatinsa na da alaƙa da ƴan bindiga.
Jaridar DAILY POST ta ruwaito cewa, akwai wani jawabi da ke yawo a kafafen sada zumunta wanda ke nuna zargin yadda gwamnatin ke biyan ƴan ta’adda.
Saidai a wani ɓangare kuma, gwamna Dauda Lawal ya zargi ƙaramin ministan tsaron da hannu a ayyukan ta’addanci, ya na mai cewa Matawalle ya kan bai wa ƴan ta’adda kariya da kuma bai wa wasu mafaka a gidan gwamnatin jihar.
Dauda Lawal ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na TVC inda ya buƙaci Matawalle ya ajiye muƙaminsa na ƙaramin ministan, ya na mai cewa ire-iren su ba su dace da kula da ragamar tsaro na ƙasa ba.
Cikin wata takarda da Sani Shinkafi ya fitar, ya yi kira ga al’umma kan kar su yaudaru ko a ruɗe su da maganar gwamnan inda ya bayyana hakan a matsayin zancen karerayi, banbancin siyasa da kuma daɗin mulki da ke ɗibar gwamnan.
Ya kuma yi kira a gare shi da ya gaggauta fitowa gidajen jaridu ya janye kalamansa akan ministan wanda ya ce Shugaba Bola Tinubu ya naɗa shi ne bisa cantatarsa ba raɗin kansa ba don shawo kan matsalolin taɓarɓarewar tsaro a Nijeriya.
“…. Matawalle, musulmin kirki, a bainar jama’a ya riƙe Alkur’ani Mai Tsarki a gidan Gwamnati da ke Gusau kuma ya rantse cewa bai da alaƙa da ƴan bindiga”, inji Shinkafi.
