INEC ta shigar da sama da kaso 88 na sakamakon zaɓen Edo a IReV

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC ta shigar da sama da kashi 88 na sakamakon zaɓen gwamna da ke gudana a jihar Edo a sahfinta na yanar gizo (IReV).

Cikin mazaɓu 4,519, INEC ta samu shigar da sakamakon mazaɓu 3,995 zuwa ƙarfe 6:40 na yamma a ranar Asabar.

A ranar 21 ga watan Satumba ne al’umma ke gudanar zaɓen kujerar gwamnan jihar ne kasancewar wa’adin gwamna mai ci, Godwin Obaseki na shekaru takwas zai ƙare a ranar 12 ga watan Nuwamba, 2024.

Jihar Edo na ɗaya daga cikin jihohin da ke gudanar da zaɓen gwamna a wani lokaci da ba na babban zaɓe ba da dokar ƙasa ta ware kasancewar akwai batutuwan hukuncin kotu da makamantansu a ire-iren ta. Sauran jihohi masu irin haka sun haɗa da; Anambara, Bayelsa, Ekiti, Imo, Kogi, Osun da Ondo.

Cikin masu zaɓe 2,629,025 da INEC ta yi wa rijista a jihar, guda 2,249,780 wato kaso 85.57 su na da katin zaɓe.

By Babaji