
Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Ranar 21 ga watan Satumbar kowacce shekara, ita ce Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware a matsayin Ranar Zaman Lafiya ta Duniya.
Ranar na mayar da hankali ne wajen kawo mafita kan tashe-tashen hankula da a ke fama da su na banbancin addini, yare da kuma ƙabilu a faɗin duniya.
Sai dai, bikin a bana ya zo lokacin da ake tsaka da fama da matsalar rashin tsaro a sassan ƙasar nan musamman na hare-haren ƴan bindiga da garkuwa da mutane.
Shugaba kuma Babban Kwamandan Ƙungiyar ƴan Sintiri ta Nijeriya (VGN), Kyaftin na sojan ruwa (mai ritaya), Abubakar Umar Bakori ya shawarci al’ummar Nijeriya da su zauna lafiya da juna, kuma su guji duk wata hanyar tashin hankali.
Kwamandan ya yi wannan kiran ne a yayin tattaunawarsa da manema labarai domin tunawa da Ranar Zaman Lafiya ta Duniya a Jihar Kaduna, ranar Asabar.
Ya yi nuni da cewa, zaman lafiya da juna shi ne abu mafi muhimmanci domin tabbatar da ci gaba cikin sauri a cikin al’umma.
Kyaftin Bakori ya ƙara cewa, “Babu abin da tashin hankali ke haifarwa face talauci da yunwa, don haka ya kamata mu zauna lafiya, mu daina kashe kawunanmu.”
Ya ce, “akwai lokacin da mu ke cikin talauci a Arewacin Nijeriya, amma duk faɗin ƙasar ana yi mana kallon cewa mu ne masu kuɗin Nijeriya, saboda muna zaman lafiya da juna. Don haka, ya kamata mu tashi tsaye mu dawo da wannan zaman lafiyar.”
Ya cigaba da cewa, “Mu na da yara a cikin ƙungiyar ƴan sintiri fiye da mutum miliyan ɗaya, waɗanda a shirye su ke su shiga duk inda aka umarce su a lungu da saƙo domin tsare rayukan al’umma.”
Ya kuma ce, waɗannan ƴan sintiri sun san ko ina kamar yadda ƴan ta’adda suka sani, domin kowannen su na aiki ne a mahaifarsa, ba a kai mutum wani wuri na daban ba.
“Me ya sa gwamnati ba za ta yi amfani da waɗannan yara ba wajen magance ƴan ta’adda? Sai dai ka ji gwamnoni na fitowa suna cewa sun kashe maƙudan kuɗaɗe wajen ƙaddamar da wata ƙungiyar tsaro, maimakon taimaka wa waɗannan jaruman yara waɗanda ba sa buƙatar ko kobo daga hannun wani”, inji shi.
Kyaftin Bakori ya yi alwashin cewa, idan har ƴan sintiri sun samu goyon baya da kayan aikin da su ke buƙata, to tabbas za a nemi ƴan ta’adda a rasa, ya na mai cewa su ba aljanu ba ne, mutane ne.
Ya ƙara da cewa, “Idan har da gaske gwamnati na son kawo ƙarshen matsalar tsaro, ya kamata ta ƙarfafa waɗanan yara, domin a shirye su ke su tunkari ƴan ta’adda”, inji Bakori.
“Ya kamata a lura cewa waɗanan yara yawancin su manoma ne, ƴan kasuwa da kuma ƴan farauta, don haka ba wai su na neman aikin gwamnati ba ne.”
Ya jaddada buƙata da muhimmancin zaman lafiya inda ya ce a shirye ya ke ya yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da zaman lafiya wanda dole sai da taimakon gwamnati.
