
Daga BELLO A. BABAJI
Majalisar Dattijai ta tabbatar da naɗin Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun a matsayin sabuwar Alƙalin Alƙalan Nijeriya, CJN.
Shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio shi ya yi hukuncin bayan sauraron bayanan tabbatarwar daga kwamitinsa kan batun, a ranar Laraba, 25 ga watan Satumba, 2024.
Kekere-Ekun ita ce Alƙali ta 23 ta hawa kan kujerar muƙamin kuma mace ta biyu a irin muƙamin.
