Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
An rantsar da Rt. Hon. Abdullahi Yusuf Ata a matsayin sabon Kwamishinan Tarayya na Hukumar ƙarɓar ƙorafe-ƙorafe na ƙasa reshen Jihar Kano.
Sabon kwamishinan wanda tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kano ne wanda ya wakilci ƙaramar Hukumar Fagge a majalisar dokokin jihar Kano har karo uku, jigo ne a jam’iyyar APC a ƙaramar hukumar Fagge.
An rantsar da Rt. Hon. Yusuf Abdullahi Ata ne a Babban Birnin Tarayya Abuja ranar Laraba, ya zama kwamishinan hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe na ƙasa reshen Jihar Kano (Commissioner Of Public Complaint Commission Kano State).
A wata sanarwar da shugaban matasa na jam’iyyar APC na Fagge Musa Rabiu ya fitar ya ce al’ummar Fagge na murna da wannan matsayi da aka ba shi domin jagora ne da kullum yake tallafa wa cigaban al’umma.
