
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Jam’iyyar adawa ta PDP a Jihar Katsina ta dakatar da sabon zaɓaɓɓen shugabanta na ƙaramar hukumar Katsina, Alhaji Ibrahim Galadima.
A cikin wata sanarwa da kwamitin jami’yyar ya fitar wanda Abba Ila Rafin-Daɗi ya sanya wa hannu aka raba wa manema labarai a Katsina, ya ce PDP ta na zargin Alhaji Ibrahim da almubazzaranci da kuɗin jam’iyyar da wasu zarge-zarge da kwamitin da uwar jam’iyyar ta kafa zai bincika.
Wannan shine karo na biyu da uwar jam’iyyar take dakatar da jiga-jigan ƴaƴanta a jihar.
A kwanaki ne jam’iyyar a matakin gunduma ta dakatar da tsohon Sakatarenta na ƙasa, Sanata Umar Ibrahim Tsauri daga jam’iyyar.
Dama tun baya jam’iyyar ta tsage gida biyu a jihar inda aka samu ɓangaren Sanata Lado Ɗanmarke da na tsohon Sakataren gwamnatin jihar, Dr Mustapha Inuwa.
