Yadda aka gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a Sakkwato

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi

Bayan kammala zaɓen ƙananan hukumomi a jihar Kebbi da wata ɗaya ita ma jihar Sakkwato mai maƙotaka da ita ta bi sawun sauran jihohi da suka gudanar da zaɓuɓɓukan ƙananan hukumomi da suka soma bayan da gwamantin tarayya ta yi barazanar rikƙe kuɗaɗen da ya kamata ta sakowa jihohi da ba su aiwatar da zaɓe a ƙananan hukumomi ba zuwa wani lokacin da ta ƙayyade.

Zaɓen da aka gudanar a ranar Asabar ɗin da ta gabata an gudanar da shi cikin lumana ba tare da wani tashin hankali ba inda Jam’iyyar APC mai mulki a jihar ta yi nasarar lashe dukkan kujerun shugabannin ƙananan hukumomi da kansilolinsu da ya ke babbar Jam’iyyar adawa ta PDP ba ta shiga zaɓen ba sai dai ƙananan jam’iyyun adawa kawai suka shiga takarar.

Duk da ya ke dai zaɓen ya kasance tuwona-maina ne jama’a sun fito tun da sassafe don jefa ƙuri’arsu saɓanin waɗansu jihohi da ke maƙotaka da jihar Sakkwato ɗin a lokacin da suka gudanar da zaɓubɓɓukan ƙananan hukumomin a baya.

Wakilinmu ya zanta da ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar mulki ta Yabo a zauren majalisar zartaswa ta jihar Sakkwato Honarabul Abubakar Shehu Yabo inda ya bayyana cewa jihar Sakkwato ta APC ce saboda haka ba abin mamaki ba ne ganin yadda mutane ke tururuwa don jefa ƙuri’arsu ba.

Ya yi kira ga waɗanda aka zaɓa da su ji tsoron Allah su yi wa mutanen nan da suka bar ayyukansu da sauran harkokinsu suka zo suka shiga layi ana ruwan sama suka zaɓe su adalci kamar yadda muka samu koyarwar siyasa daga limaminmu Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko.

Kwamishinan kuɗi na jihar Sakkwato Alhaji Muhammad Jabbi Shagari ya yabawa ma’aikatan hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Sakkwato bisa ga yadda ta tsara gudanar da zaɓen tare da kai kayan aiki cikin lokaci, d kuma jami’an tsaro da bisa ga zirga-zirga da suka yi tun daren Juma’a har zuwa lokacin da aka kammala zaɓen kuma ba a sami wani tashin hankali ba.

Ya ƙara da cewa tun kafin wannan lokacin gwamantin jihar Sakkwato ta ja ɗamarar daƙile duk wata barazanar tsaro kuma Alhamdu lillah ba a sami barazana kowace iri ba har aka kammala zaɓen.

Haka-zalika ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar mulki ta Shagari Honarabul Barista Maidawa ya gode wa Allah da ya nuna musu wannan ranar da suka daɗe suna jira don auna dangantakar wannan gwamanti da al’ummar da ta ke jagoranci, yanzu kowa ya ga irin kyakykyawar alaƙar da ke akwai wanda waɗansu mutane tun da asuba suke a mazaɓun su don sauke nauyin da ke kansu.

Wannan gwamnatin ta Maigirma Ahmed Aliyu gwamnati ce mai baiwa kowa haƙƙinsa saboda haka mutanen da ake so su take baiwa takara.

Wani ɗan jam’iyyar adawa ta PDP da ya nemi a sakaya sunansa saboda a cewarsa jam’iyyar su ta ƙaurace daga shiga zaɓen ƙananan hukumomin saboda haka ba abinda za su ce, amma dai a wajensa ba zaɓe ba ne wannan illa dai sun yi naɗe-naɗe ne na waɗansu mutane.

Ya ƙara da cewa ai ko waɗannan ƙananan jam’iyyun adawa da ka gani sun shiga zaɓen ai gwamnati ce ta ɗauki nauyinsu. 

By ukarofi