Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnatin Umar Namadi na Jihar Jigawa, ta amince da ware kuɗi har Naira N26,274,553,600.00 don sayen tantan ɗin noma guda 300, garmar huɗa guda 300, garmar noma guda 300, garmar ‘disc ridger’ guda 300, bodin tantan (Tipping Trailer) guda 300, injin shuka guda 150, injin shuka shinkafa guda 150, motar girbin amfanin gona guda 40, da kuma na’urar feshin maganin ƙwari guda 80.
Haka kuma an ware Naira 263,160,000 don tura ma’aikata 30 zuwa ƙasar Chaina, don samun horo na tsawon watanni uku kan yadda za su riƙa kula da kuma gyaran sababbin na’urorin da za a samar.
Za a kafa cibiyoyi 60 da za a ajiye waɗannan kayan aiki a faɗin jihar, inda za a samar da cibiyoyi biyu a kowacce daga mazaɓun ‘yan majalisar jiha guda 30, sannan kowanne ɗaya daga cikin waɗannan ƙwararrun ma’aikata zai riƙa kula da cibiyoyi biyu.
Wannan shiri zai samar da ayyuka yi ga matasa 2,700, kuma zai ƙara yawan ayyukan yi yayin da aikin ke cigaba.
Majalisar Zartaswar Jihar Jigawa ce ta amince da haka a Taron Majalisar Zartaswa na ranar Alhamis, wanda ya gudana a Gidan Gwamnatin Jihar Jigawa, wato Dutse a ranar 19 ga Satumba.
Majalisar ta kuma amince da sakin kuɗi har Naira N8,194,918,000.00 don biyan kaso 30% na kuɗin kayan aiki da kuma horar da malaman gonar guda su talatin.
A zaman majalisar har yau dai, an amince da bayar da kuɗi Naira biliyan 2.559, domin ayyukan gini, gyara, sayen kayan aiki da tsaftar makarantun firamare na faɗin ƙananan hukumomin Jigawa guda 27.
Haka kuma an amince a ware Naira biliyan 1.053, domin bayar da kwangilar aikin gyaran makarantu na firamare da ƙananan makarantun sakandare na faɗin Jihar Jigawa.
Sannan kuma an sanya hannu kan yarjejeniyar kafa cibiyar horas da ɗalibai ta musamman, wadda ƙungiyar ƙwararrun Akantoci ta Nijeriya (ICAN) za ta gina a Dutse, a matsayin haɗin guiwa tsakanin ICAN da Gwamnatin Jihar Jigawa
