Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnatin Jihar Kano ta samu rancen Naira biliyan 177.4 daga Hukumar Raya kasar Faransa gina sabbin matatun ruwa a Tamburawa da inganta samar da ruwan sha.
Gwamna Abba ya ce aikin na da nufin inganta hanyoyin samun ruwan sha, duba da ƙaruwar al’ummar jihar cikin hanzari.
Abba ya jaddada muhimmancin aikin, wanda ya ce fuskanci tsaiko sakamakon annobar COɓID-19 da sauran ƙalubale, amma yanzu ana sa ran kammala shi nan da shekaru biyu masu zuwa.
Ya ce za a gudanar da aikin ne a ƙarƙashin shirin sake fasalin ruwan birane na ƙasa, kuma ma’aikatar albarkatun ruwa ta tarayya ta ba da tabbacin hakan.
Gwamnan ya bayyana haka ne ta bakin Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Ali Haruna Makoda, yayin wani taron bitar ayyuka na kwanaki biyu da aka gudanar a Kano, wanda ya samu halartar wakilai daga jihohin Filato, Enugu, da Ondo.
Manajan Daraktan Hukumar Ruwa ta Jihar Kano, Garba Ahmad Bichi, ya bayyana cewa, aikin ya haɗa da gina sabuwar ma’ajiyar ruwa mai ɗaukar lita miliyan 250 a kowace rana, wanda zai magance matsalar ƙarancin ruwan da ake fama da ita a cikin birnin, sakamakon karuwar al’umma.
