Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Kimanin ‘yan ƙungiyar Daesh 20 ne suka nutse a ruwa a lokacin da suke ƙoƙarin tsallakawa wani kogi da ke kan iyakar Nijeriya da Jamhuriyar Nijar.
Lamarin ya faru ne a tsakanin yankin Kafetoa da Bulabulin Gaidam a jihar Yobe a Nijeriya, a cewar wani masani kan yaƙi da ta’addanci, Zagazola Makama.
Rahotanni sun ce maharan na kan hanyarsu ta zuwa ƙauyen Tam da ke jamhuriyar Nijar, kusa da unguwar Kannamma da ke jihar Yobe, inda wata igiyar ruwa mai ƙarfi ta tafi da su, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarsu.
Makama ya bayyana cewa an raba ‘yan ta’addan ne daga wasu muhimman wurare da suka haɗa da Bulabulin Geidam, Chettimari, da Diffan da ke kan iyakar Nijeriya da Nijar.
ƙungiyar ISWAP ta kasance jigo a fagen tada ƙayar baya a yankin arewa maso gabashin Nijeriya. A baya-bayan nan dai ƙungiyar na fuskantar matsin lamba daga zafafan hare-haren sojojin Nijeriya da nufin daƙile ayyukansu.
A wani hari na daban, ƙungiyar Boko Haram mai alaƙa da ISWAP ta kashe fararen hula da dama tare da ƙona shaguna da gidaje a wani ƙauye na Yobe, lamarin da ke nuna ƙalubalen tsaro da ake ci gaba da fuskanta a yankin.
