
Daga BELLO A. BABAJI
Wani ɗan gwagwarmaya mai suna Martins Otse da aka fi sani da ‘VeryDarkMan’ ya bayyana yadda ya haɗu da Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo.
Ɗan gwagwarmayar ya yaba wa ministan kan dakatar da wasu jami’an gidan yari da ake zargin su da hannu a lamarin Bobrisky.
Ya ce, ministan ya yi hakan ne don mayar da Nijeriya waje mai tsafta, ya na mai cewa hakan zai samu ne ta hanyar ƙoƙarin da ake yi a matakin da mutum ya tsinci kan sa.
Hakan na zuwa ne jim-kaɗan bayan wata ɗaukar murya da ya fitar game da lamarin cin-hanci na Bobrisky da ya haifar da cecekuce a cikin al’umma.
VeryDarkMan ya saki ɗaukar ne inda ake zargin Idris Ukuneye da aka fi sani da Bobrisky da bai wa wasu jami’an EFCC cin-hancin Naira miliyan 15 don su ajiye batun tuhumar badaƙalar kuɗaɗe akan sa.
An kuma zarge shi da bai wa wasu jami’an Hukumar Gyaran Hali ta Ƙasa (NCos), cin-hanci game da zama a gidan yari waɗanda tun lokacin aka dakatar da su.
