
Daga BELLO A. BABAJI
Jami’an hukumar hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta’annati, EFCC sun kama tsohon gwamnan Jihar Taraba, Darius Ishaku kan zargin badaƙalar Naira biliyan 27.
Rahotanni sun bayyana cewa an kama Ishaku ne, wanda ya sauka a kujerar gwamnan Taraba a shekarar 2023 bayan shafe shekaru takwas, a gidansa da ke Abuja a safiyar ranar Juma’a.
Har zuwa daren ranar, tsohon gwamnan na ofishin hukumar inda wata majiya ta ce ana tuhumar sa ne da laifuka 15 wanɗanda da zarar an samu hujjoji akan sa, za a miƙa shi ga kotu.
Majiyar ta ƙara da cewa, tun bayan saukar sa daga kujerar gwamnan, EFCC ke bincike akan sa sakamakon kuɗaɗe da dama da ake zargin sauya akalarsu.
Kakakin hukumar, Dele Oyewale ya tabbatar da batun wanda daga nan bai ƙara wanɗansu bayanai ba.
Hakan na zuwa ne yayin da EFCC da tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ke cigaba da takun saka a tsakanin su game da tuhumar badaƙalar kuɗi da aka masa.
