Babban Hafsan Tsaron Nijeriya ya yi wa gwamnan Akwa-Ibom ta’aziyyar rasuwar matarsa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Babban Hafsan Tsaron Nijeriya (CDS), Janar Christopher Musa, ya aika saƙon ta’aziyyarsa ga Gwamnan Jihar Akwa-Ibom, Umo Bassey Eno da al’ummar jihar kan rasuwar matarsa, Misis Patience Umo Eno.

Daraktan Labarai na Hedikwatar Tsaro, Janar Tukur Gusau ya fitar da hakan cikin wata takarda a ranar Juma’a inda Janar Musa ya bayyana alhininsa game da rashin wanda ya ce hakan wani muhimmin giɓi ne ga iyalan gwamnan da ma al’ummar jihar baki ɗaya ganin yadda ta ke bada gudunmawa wajen tafiyar da harkokin gwamnatin jihar.

Janar Musa ya kuma jinjina wa kyawawan halayenta, ya na mai cewa ba iya matar gwamnan ta zama ba, har ma amintacciyar ta hannun dama ga gwamnan ta kasance.

Ya ce, za a cigaba da tunawa da ƙoƙarinta na inganta rayukan yara, matasa da sauransu a shirye-shiryen da ta samar.

Ya kuma yi kira ga ahalin marigayiyar da ma al’ummar jihar su kasance masu juriya game da babban rashin da ya same su.

By Babaji