Ƙaramar Hukumar Fagge na ƙoƙarin ganin ta fita daga sahun masu ɗauke da cutar Shan Inna

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Shugaban kula da sashen lafiya a matakin farko na ƙaramar hukumar Fagge, Malam Ahmad ɗahiru ya bayyana cewa ƙaramar hukumar na matuƙar ƙoƙarin ganin ta fita daga jerin ƙananan hukumomi dake ɗauke da cutar shan Inna.

Ya ce a wannan karon na zagayen allurar riga-kafin cutar akwai buƙatar sanya ido sosai domin ƙaramar hukumar ta Fagge ta tsinci kanta cikin waɗanda ke ɗauke da cutar wacce aka samu a cikin ruwa. 

Ya ce duk jihar Kano Fagge ce ke ɗauke da ƙwayar cutar mafi rinjaye kuma sun sami tallafi daga Gwamnatin jihar Kano ta ba su ma’ajiyar magunguna riga-kafin sannan ƙaramar hukuma ta tallafa musu da babban firinji domin ganin an cimma samun nasarar aikin.

Malam Ahmad ɗahiru ya yi nuni da cewa kasancewar Fagge na ɗauke da manyan kasuwanni da suka kewaye ta hakan kan haifar da samun matsaloli da suka shafi lafiya a Fagge amma sun ɗauki tanadi na ma’aikata na musamman da suke aiki a kasuwanni da tashoshin motoci baƙi da suke shigowa ana kula da su wajen yi musu riga-kafi.

Ya ce akwai ƙungiyoyi da dama da suke aiki da su da suke bayar da gudunmawa wajen ganin an samu nasarar kawar da cutar ta Shan Inna a ƙaramar hukumar.

Malam Ahmad ɗahiru ya yaba wa masu ruwa da tsaki na yankin da masu sarautar gargajiya da iyaye da malamai bisa goyon baya da suke bayarwa domin cimma nasarar yaƙi da cutar ta shan Inna da sauran cututtuka.

By ukarofi