Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnatin Jigawa ta haɗa guiwa da kamfanin Safa & Fresh domin kafa cibiyoyin maida motoci masu amfani da gas a jihar.
Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ce gwamnatin tarayya za ta tallafa wa jihohin ƙasar nan 36 har da babban birnin tarayya wajen samun motocin bas masu amfani da iskar gas samfurin CNG domin sauƙaƙa wa al’umma tsadar kuɗin mota.
A cikin jawabinsa na Tunawa da Ranar Samun ‘Yancin Kan Nijeriya a ranar Talata, shugaban ya ce an kusa kammala shirin sauya fasalin makamashi.
“Muna dab da kammala shirin sauya fasalin makamashi. Muna kan fara amfani da sabon shirin amfani da iskar gas samfurin CNG a harkokin sufuri tare da haɗin guiwar kamfanoni masu zaman kansu. Gwamnatin Tarayya a shirye take ta tallafa wa jihohi 36 da wajen mallakar waɗannan motocin bas masu domin samar da rahusa a ɓangaren sufuri,” a cewar shugaban Tinubu.
A watan Agustar bara, shugaba Tinubu ya amince da ƙudirin Fadar gwamanti na amfani da iskar gas (PCNGI).
A cikin jawabin tsohon maitaimaka wa shugaban ƙasa kan yaɗa labarai, Ajuri Ngelale, ya ce samar da shirin ya nuna aniyar shugaban ƙasa na rage raɗaɗin cire tallafin man fetur ga ‘yan Nijeriya ta hanyar samar da sauƙi a ɓangaren makamashi.
A cewar Ngelale, wannan wani tsari ne na sauya fasalin harkar sufuri a ƙasar nan wanda ake sa ran samar da sama da ababen hawa dubu 11, 500 da za su riƙa amfani da iskar gas samfurin CNG.
“A lokaci guda kuma, za a bunƙasa ɓangare ƙere-ƙere na cikin gida da samar da ayyukan yi kamar yadda yake cikin manufofin wannan gwamnati,” kamar yadda Ngelale ya tabbatar.
A watan Yulin da ta gabata, kamfanin mai na ƙasa, NNPCL, da na Kamfanin Iskar gas, NIPCO, sun ƙaddamar da tashoshi 12 na samfurin wannan iskar gas ɗin wanda ƙaramin minitan man fetur na ƙasa, Ekperikpe Ekpo, ya tabbatar da cewa wannan yunƙuri ne na gwamnati wajen assasa wannan shiri.
Haka kuma, a ranar 26 ga watan Satumbar, mai taimaka wa shugaban ƙasa kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, a yayin da yake zantawa da manema labarai a gidan gwamnati, ya ce gwamnatin tarayya ta ɓullo da wannan shiri na na amfanin da isgar gas ɗin CNG ne domin rage tsadar makamashi ga masu ababen hawa.
Kuma a cewarsa tuni a wasu jihohi kamar Legas da Ibadan da Benin da sauran wurare al’umma suka fara yin na’am da wannan nau’i na iskar gas saboda irin sauƙin da yake da shi idan aka kwatanta da man fetur.
