Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta kama wata mata da ake zargin ta mayar da gidan da ta karɓa haya amma ta maida shi wajen saukar baƙi, maza da mata suna aikata baɗala.
Muƙaddashin Babban Kwamandan Hisbah na jihar Kano, Dakta Mujahid Aminudeen ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da hukumar ta aike wa Manhaja a ranar Lahadi.
Ya ce an kama matar a unguwar Samegu bayan mazauna unguwar sun kawo ƙorafin ta’adar da ta ke yi.
Hakazalika Dakta ta kama wasu ‘yan mata a titin Filin Sukuwa da ake zargin ana ɗaukarsu ana kai su otel domin yin lalata da su.
Ya kuma ƙara da cewa jami’an Hisbah sun kama har da masu juna biyu da masu goyo a cikin matan.
“A ci gaba da ayyukan hukumar Hisbah na tsaftace jihar kano daga aikata baɗala cikin yardar Allah yau hukumar ta kai sumame unguwar titin filin sukuwa inda wasu yara ‘yan mata suke aikata baɗala, ana ɗaukarsu ana kaisu otel ana lalata da su.
“A cikin su har da masu ciki da masu goyo, haka kuma an cafke wata mata da ta maida gidanta mafakar baɗala inda take ba su hayar ɗakinta a unguwar Samegu an kamata da maza 3 mata 3 haka, ana yin bincike a kanta don gano mutanen da suka bata hayar gidan,” inji sanarwar.
Ya ce kamen wani ci gaba ne na ‘Operation Kauda Baɗala’ da runudnar ke yi don gyaran tarbiyya a jihar.
