Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamna Dikko Raɗɗa ya sanar da cewa gwamnatinsa ta kashe Naira biliyan uku da miliyan saba’in da bakwai wajen kiyon lafiya a faɗin jihar.
Gwamnan ya yi wannan magana ne a lokacin da yake buɗe cibiyar masu ɗauke da ciwon sikila da Uwargidan Gwamnan Hajiya ɗulaihah Umar Dikko Raɗɗa ta assasa a babban asibitin Katsina.
Ya ce kuɗaɗen an kashe su ne wajen biya wa ɗaliban koyon karatun kiyon lafiya suke a ciki da wajen Nijeriya.
Malam Dikko Raɗɗa ya bayyana cewa gwamnati ta biya tallafin kuɗi naira miliyan 112 ga ɗalibai 542, da kuma faɗaɗa ƙananan asibitoci guda 102.
Ya kuma sanar da cewa gwamnatin Katsina nan bada jimawaba za ta faɗaɗa wasu ƙananan asibitoci guda 34 zuwa manyan asibitoci a faɗin jihar .
Uwargidan Gwamnan Hajiya Zulaihah Umar Dikko Radda wanda ta assasa cibiyar ƙarƙashin ƙungiyar ta SASHIN ta ce cibiyar zai bada magani na masu ɗauke da cutar Sikila da na farar masassara watau Maleriya a duk bayan wata ɗaya kyauta .
Ta kuma ƙara da cewa nan bada jimawa ba ƙungiyar ta za su assasa irin wannan cibiyar a shiyyar Funtuwa da Daura.
Uwargidan gwamnan ta sanar da cewa a yanzu haka akwai mata guda dubu 9 da ke ɗauke da cutar Sikila a jihar da ke karɓar magani a cibiyar da ƙungiyar ta ke ɗaukan nauyi.
Kwamishinan lafiya na jihar Alhaji Musa Adamu Funtuwa yabawa gwamna Dikko Raɗɗa ya yi bisa ƙoƙarinsa na inganta harkar kiwon lafiya a jihar.
