Cin zarafi: An yanke wa wani ɗan Lebanon hukuncin shekaru 14 a kurkuku a Kano

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Wata babbar kotun tarayya da ke Jihar Kano ta yanke wa wani ɗan ƙasar Labanon, Zuhier R. Akar mai shekaru 67 hukuncin zama a gidan yari na tsawon shekaru 14 sakamakon lalata wasu yara mata biyu.

Hukumar hana fataucin ɗan-adam (NAPTIP) reshen jihar, ta tsare Aktar ne wanda ke zama a yankin Gidan Wanka da ke ƙaramar hukumar Fagge da laifuka biyu da ke da alaƙa da lalata.

A lokacin gudanar da hukuncin, Mai Shari’a S. M. Shua’ibu ya ce an tabbatar da wanda ake tuhuma da aikata laifin inda ya zartar masa da hukuncin zama a kurkuku na shekara 14 ba tare da zaɓi na biyan tara ba.

Sannan, alƙalin ya kuma umarce shi ya biya tarar Naira miliyan 2 ga aikata laifin.

A ranar 5 ga watan Satumba, 2024 ne hukumar ƴan sandan farin kaya ta DSS ta ruwaito batun ga NAPTIP.

Wata ɗaukar bidiyo ta nuna yadda tsohon ke lalata da wasu ƴan mata biyu masu shekaru 14 da 15 a gidansa da ke unguwar Gidan Wanka.

By Babaji