Halin da Nijeriya ke ciki ba daga Tinubu ba ne – Matar shugaban ƙasa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Matar shugaban ƙasa, Sanata Remi Tinubu ta ce halin da Nijeriya ke ciki a yanzu, ba mijinta Shugaba Bola Tinubu ba ne ya haddasa.

Ta ce, mijin nata ya duƙufa ne wajen samar da daidaito ga al’amuran da suka taɓarɓare a Nijeriya a cikin shekaru biyu da ya ke kan mulki.

Ta bayyana hakan ne a Fadar Ooni Ile-Ife ta jihar Osun a lokacin da ta kai ziyara ga sarkin inda daga bisani da ƙaddamar da aikin titi mai tsawon kilomita 2.7 da kuma buɗe wajen taro da aka sanya wa sunanta a jami’ar Obafemi Awolowo.

Sanata Remi ta ce, yanzu ne gwamnatinsu ke cikin shekara ta biyu inda ta ce ba su suka jefe Nijeriya halin da take ciki ba, don haka mijinta ke ƙoƙari wajen ganin an gyara al’amura don gobe mai kyau ga al’umma.

Haka kuma, ta ce su na sane da cewa an cire tallafin fetur, ta na mai cewa nan da shekara biyu Nijeriya za ta inganta sama da wannan lokaci.

Kazalika, ta yi kira ga matasa su kasance masu jajircewa tare da riƙe sana’o’i don dogaro da kai inda ta ce a matsayinta na mai shekaru 64, har yanzu ta na aiki.

Har’ilayau, matar shugaban ƙasar ta yi kira ga al’umma su cigaba da haƙuri saboda akwai fatan Nijeriya za ta samu ci-gaba nan da wani ɗan lokaci.

By Babaji