
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Hukumar tsaro ta Civil Defence ta ƙara wa jami’anta a da ke faɗin Nijeriya girma a matakai daban-daban, inda a jihar Katsina jami’ai 167 suka samu shiga cikin sahun.
Cikin waɗanda suka sumu ƙarin girman akwai mai magana da yawun hukumar a Katsina, DSC Buhari Hamisu wanda ya zama SC Buhari Hamisu a yanzu kamar yadda ya bayyana a wata takarda.
Ya ce, nan ba da jimawa ba za a yi bikin ƙarin girman a hedikwatar hukumar ta jihar Katsina.
