Tsohon alƙali ya gurfana bisa cin zarafin makauniya matar aure

Spread the love

Masu buƙata ta musamman sun yi dafifi a kotun majistaren Zariya

Daga MOH’D BELLO HABIB a Zariya

An gurfanar da wani tsohon alƙali a gaban kotu bisa zargin cin zarafin wata makauniya matar aure a Jihar Kaduna, lamarin da ya hankalin al’umma, musamman masu buƙata ta musamman da suke yankin da abin ya faru.

Wata kotun Majistare da ke Tudun Wada a Zariya ta Jihar Kaduna ta ɗage ci gaba da sauraron ƙarar wani tsohon alƙalin Babbar Kotun Shari’ar Musulunci, Mahmouda  Shehu, kan zargin cin zarafin wata matar aure makauniya mai suna Sa’adiyya Muhammed  a ranar 11 ga Nuwamba, 2024, domin cigaba da shari’ar

An gurfanar da tsohon Alƙali Mahmoud Shehu a gaban kotun majistare da ke Tudun Wada a Zariya bisa zargin keta haddi da nuna ƙarfi da kuma cin zarafin matar, wacce maƙociyarsa ce da suke zaune a gidan haya ɗaya da shi.

Dan sanda mai gabatar da ƙara, Sufeto Adamu Abubakar, ya shaida wa kotu cewa, a ranar 6 ga Satumba, 2024, wani mutum mai suna Garba Adɗa’u, wanda mijin matar ne, ya kai ƙorafi ofishin ’yan sanda da ke Tudun Wada Zariya cewar wanda ake tuhuma bisa zargin rufe babbar ƙofar gidan da suke haya tare da shi, inda ya bi matar tasa har ɗakinta ya buge ta sa’annan kuma ya bugi ƙarin mutanen biyu, waɗanda ke zama da ita.

Mai gabatar da ƙarar ya cigaba cewa, kamar yadda mijin matar ya shigar a ofishin ’yan sandan, sakamakon dukan da aka yi zargin wanda ake tuhuma cewar ya yi, sai da aka kai matar asibiti, domin duba lafiyarta.

Sufeto Abubakar ya ce, hakan ya saɓa wa sashe na 327 da 237 da 239 da kuma na 201 na kundin laifuffuka na Jihar Kaduna.

Lauyoyin wanda ake ƙara, SM Abubakar da Ibrahim B. Ahmed, sun nemi kotu ta sanya masu wata rana, saboda ɓangaren masu ƙara su samar masu da wasu takardun bayanan tuhume-tuhumen da ake yi wa wanda suke karewa, saboda su fahimci inda aka sa gaba.

Mai Shari’a Majistare Lukman Sidi ya amince da ranar 11 ga Nuwamba, 2024, a matsayin ranar da za a ci gaba da sauraron ƙarar, kamar yadda lauyoyin suka roƙa.

Da ya ke bayyana takaicinsa a game da abin ya faru, shugaban ƙungiyar masu buƙata ta musamman reshen Jihar Kaduna, Barista Ibrahim Sani Zubairu, ya ce, ƙungiyarsu ta ji labarin irin cin zarafin da tsohon alƙalin kotun Shari’ar Musulunci ya yi wa ɗaya daga cikinsú.

Ya ce, sun halarci zaman kotun ne domin a yi komai a gabansu, saboda kasancewar wacce ya aikata laifin nan masanin shari’ar Musulunci ne.

Ya ce, abinda ya aikata laifi ne babba, saboda makauniya ce kuma matar aure, wacce doka ba ta yarda da abinda ya aikata.

By ukarofi