Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Fitaccen marubucin adabi, Farfesa Wole Soyinka, ya ce, ya amince a kira shi wanda bai yarda akwai Allah ba, kuma ya bayyana dalilin da ya sa ya fi son addinin Orisa na gargajiya.
A yayin da ya ke bayyana hakan a wata hira da ya yi da Larry Madowo na CNN a baya-bayan nan, fitaccen marubucin adabin ya ce zurfin imani a Musulunci da Kiristanci bai dace da bautar Orisa da yake yi ba, ya ƙara da cewa Orisa ya fi burge shi.
A cewarsa, bautar Orisa na ɗaya daga cikin addinan Afirka da ke guje wa tashin hankali kuma sun yi ƙirƙire-ƙirƙire.
“Na yi sa’a da aka haife ni a cikin duniya biyu – duniyar Kirista da masu bautar Orisa na gargajiya. Kakana an haife shi a Kiristanci ne amma ya mutu yana Orisa kuma sarki ne,” inji shi.
Ya ƙara da cewa, “A gare ni, bautar Orisa ta fi fasaha, kuma ta fi burge ni. Ban samu wani abu mai ban sha’awa ba a cikin Kiristanci ko Musulunci, wanda hakan ya sa ban girma tare da Musulmai ba.
Wannan ba shi ne karo na farko da marubucin adabin ya bayyana ra’ayinsa a kan addini ba. Isan dai ba a manta ba, a shekarar 2022, a lokacin da yake gabatar da tarin ƙasidunsa, ya ce ba ya buƙatar wani addini, kuma ba ya bauta wa wani abin bauta, lura da cewa shi ba Kirista ba ne shi kuma ba Musulmi ba.
