Mun gina matatarmu ne babu tallafin gwamnati – Ɗangote

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote a ranar Talata ya bayyana cewa an gina matatar man Dangote ba tare da tallafin gwamnati ba.

Ɗangote ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron ƙungiyar masu matatun mai ta Nijeriya, CORAN, a Legas.

Taron dai yana da taken, “Mayar da Nijeriya a matsayin mai fitar da albarkatun man fetur.”

Ɗangote, wanda ya samu wakilcin Ahmed Mansur, rukunin Dangote, ya ce akwai buƙatar ƙarfafa gwiwar masu zuba jari don cimma burin ƙasar nan na zama cibiyar tace mai ta duniya.

Ya jaddada muhimmancin tabbatar da wadatar kayan abinci, tare da yin kira da a kawo ƙarshen ƙarancin ɗanyen mai.

“Abin takaici ne a yayin da ƙasashe irin su Norway ke saka hannun jarin kuɗaɗen su a ɓangaren man fetur, mu a Afirka muna kashe kuɗaɗenmu ta wasu ɓangare na daban,” inji Dangote.

Ya kuma yi kira da a ba da fifiko wajen aiwatar da ayyukan samar da ɗanyen mai a cikin gida da kuma faɗaɗa ƙarfin samar da ɗanyen mai don biyan buƙatun sabbin wuraren tace man.

Ɗangote ya yaba da ƙoƙarin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi, inda ya bayyana irin matakan da gwamnati ke ɗauka na ƙara haɓaka kamfanonin mai na ƙasa da ƙasa, IOC, karkatar da kayayyaki da sauran tsare-tsare.

Duk da kasancewar ƙasar da ta fi kowacce fitar da ɗanyen man fetur a nahiyar Afirka, Dangote ya bayyana cewa Nijeriya ta daɗe tana dogaro da shigo da man fetur domin biyan buƙatunta na tace mai.

Ya ce, “Nijeriya na shirin rikiɗewa daga “mai shigo da kayayyaki” zuwa “mai fitar da kayayyaki” masu tace kayayyaki, inda ta sanya kanta a matsayin mai taka muhimmiyar rawa a kasuwancin duniya.

“Wannan sauyi da ke tafe yana nuni da ci gabanmu a matsayin masana’antu da kuma kasa baki ɗaya. Muna godiya ga Shugaba Tinubu bisa goyon bayan da ya ba mu a tsawon wannan tafiya.”

Dangote ya kuma yi tsokaci kan irin damarmakin da ake samu a nahiyar Afirka, inda ya bayyana cewa, a kullum nahiyar na shigo da ganga miliyan uku na albarkatun man fetur, inda rabin wannan ke fitowa daga ƙasashen da ke gabar teku.

Ya ƙara da cewa, wadannan kasashe suna haƙo sama da ganga miliyan 3.4 na ɗanyen mai a kullum, waɗanda ake shigo da su daga ƙasashen Turai, Rasha da sauran yankuna.

“A shekarar 2023 kaɗai, an kiyasta wannan ciniki da ya kai kusan dala biliyan 17.

“Duk da haka, waɗannan kasuwanni za su fi dacewa daga Nijeriya, tare da rage farashin kayan aiki da baiwa ƙasashe damar sayen buƙatunsu na man fetur a kan lokaci,” inji shi.

By ukarofi