Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Karamin Ministan Tsaro, Bello Mohammed Matawalle, ya gargaɗi masu ba wa ’yan ta’adda bayanai cewa su tuba ko su gamu da ajalinsu.
Ya yi wannan gargaɗin ne a ƙauyen Gundumi a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa ƙananan hukumomin Isa da Sabon Birni a jihar Sakkwato domin ziyarar gani da ido a ranar Alhamis.
Ministan wanda ya nuna baƙin cikinsa kan yadda rayuwa ta koma a ƙauyen, ya ce “wannan wurin a da ya kasance yana da walwala da harkoki da dama.
“Ina tabbatar muku za ta dawo, za mu kawo wani sansanin soji a nan.
“Amma ku ji tsoron Allah, waɗanda suke ta kira da sanar da ’yan fashi game da zirga-zirgar jami’an tsaro da ma ’yan uwansu su daina daga yanzu.
“Gwamma ku tuba ko mu aika ku lahira,” in ji shi.
Aikace-aikacen ‘yan ta’adda dai ya yawaita a Arewa maso Yamma, inda ake fama da matsalar masu garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa, yayin da gwamnati da jami’an tsaro ke iƙirarin suna bakin ƙoƙarinsu don dawo da zaman lafiya a yankin.
