Mahukunta a Florida na ƙasar Amurka na ci gaba da gargaɗi game da barazanar da guguwar Milton ke yi, inda aka umurci jama’a da su kaurace wa gidajensu cikin gaggawa.
Hukumomi a Amurka sun ce a wannan Talata guguwar Milton mai lamba 4 za ta ƙara girma, yayin da ta yi barazana ga tsibirin Yucatan na ƙasar Meɗico a kan hanyarta ta zuwa Florida, inda aka umarci sama da mutane miliyan guda da su ƙaurace wa hanyarta.
Gaɓar yammacin Florida mai yawan jama’a, wanda har yanzu bata gama murmurewa daga mummunar guguwar Helene da ta afkawa mata makwanni biyu da suka gabata, na fuskantar ƙarin wata barazana a ranar Laraba.
Cibiyar kula da guguwa ta Amurka ta yi hasashen cewa, Milton na iya afkawa babban birnin Tampa Bay, mai ɗauke da mutane sama da miliyan uku.
Cibiyar ta ce, Milton za ta ci gaba da zama guguwa mai matuƙar haɗari da Florida zai fuskanta, wanda ta ce zata yi mummunar ɓarna, tare da katse wutar lantarki na kwanaki a yankin.
Ya zuwa ƙarfe 10 na safiyar Talatan agogon ƙasar, guguwar ta kilimita 105 daga Arewa maso gabashin babban birnin Jihar Yucatan na ƙasar Meɗico, kan hanyarta zuwa Florida. RFI
