Daga JAMEEL GULMA a Kebbi
Waɗansu masunta da ke sana’ar kamun kifi a kogin Neja da ke yankin Yawuri ta jihar Kebbi sun samu nasarar kashe wata dorina da ta kashe mai kula da gandun Sarkin Yawuri Dokta Muhammad Zayyanu tare da raunata wani masunci a cikin kasa da mako biyu a ƙauyen Gungun-Sarki da ke daf da garin na Yawuri.
Kisan Dorinar ya biyo bayan umarnin da gwamnan jihar ta Kebbi Malam Nasir Idris ya bayar ta bakin maimartaba Sarkin Yawuri inda ya ce a fantsama wajen farautar wannan Dorinar saboda kaucewa ƙarin hasarar rayuwa.
Alhaji Nasiru Mayanan Gungu ya bayyana cewa ranar Litinin ne aka yi wani gangamin haɗin gwiwa tsakanin masunta da manoman shinkafa da sauran masu sana’o’in da suka shafi harkokin ruwa inda aka samu nasarar kashe Dorinar bayan da ta faɗa wani tarko da aka ɗana a cikin ruwan. Bayan da ta kamu sai mutane suka fito suka kai mata farmaki da makamai da suka haɗa da zago da mashi da kibiya da dai sauran kayan fada har Allah ya sanya aka samu nasarar kashe ta.
Mayanan Gungun ya ƙara da cewa an samu nasarar kashe ɗiyar dorinar ne da ƙarfe goma sha ɗaya na safe sannan sannan daga baya zuwa ƙarfe uku na yamma aka kashe uwar. Bayan kashe Dorinar aka ɗauketa zuwa fadar Hakimin Gungu, Alhaji Kasimu Aliyu, inda aka feɗe namanta kuma aka rarraba namanta ga jama’ar yankin har ma da wasu daga garin Yawuri,” inji Mayanan Gungun Alhaji Nasir Sarki.
Al’ummar Masarautar Yawuri dai sun ji daɗi kan nasarar da aka samu ta kisan dorinar da ɗiyarta saboda ta ɗauko hanyar hallaka jama’a, sun kuma yaba wa Gwamna Nasir Idris da Sarkin da Maimartaba Sarkin Yawuri Dokta Muhammad Zayyanu Abdullahi bisa wannan mataki da suka ɗauka na bayar da umurni na hallaka wannan dorinar ita da diyarta.
Malam Sani Abacha ɗaya daga cikin shugabannin masu sana’ar sayar da kifi a yankin masarautar Yawuri ya bayyana jin daɗinsa bisa ga kisan wannan Dorinar saboda a baya ta saka zaman dar-dar a zukatan masunta saboda tunanin a kowane lokaci tana iya kai musu farmaki saboda yanzu haka Malam Usman Maigandi ɗan kimanin shekaru sittin da ta kaiwa farmaki makon da ya gabata yanzu haka yana asibitin koyarwa ta Usman Danfodiyo da ke Sokoto sanadiyyar miyagun raunuka da ta yi masa.
