Daga USMAN KAROFI
NFC ta sake jaddada aniyarta wajen inganta tsaro na zamani da yaƙi da asarar bayanan ƙididdiga a taron shirin ilimi da haɗin gwiwa na Ƙasa da Ƙasa (TNB) na hukumar musayar ilimi ta Jamus (DAAD) da aka gudanar a birnin Berlin.
Dr. Ali Nuhu, Manajan Daraktan hukumar NFC, ya gabatar da takarda mai taken “Asarar bayanai da haɗin gwiwar NFC da gwamnatin Jamus da hukumominta,” inda ya ja hankalin mahalarta taron tare da gabatar da muhimman shirye-shiryen haɗin gwiwa da NFC ke gudanarwa, ciki har da dabaru na zamani da ake aiwatarwa don kare bayanan kididdiga na bidiyo da sauti na ƙasa.
Dr. Ali Nuhu ya bayyana cewa NFC ta jajirce wajen gudanar da ayyukan kare kayan tarihi na ƙididdiga da sauti na ƙasa. Ya yaba wa gwamnatin Jamus da hukumominta saboda irin goyon bayan haɗin gwiwa da suke bayarwa wajen kare al’adun bidiyo da sauti na Nijeriya, wanda ake gudanarwa a NFC ta hanyar ajiyar kayan tarihi, mayar da su cikin zamani, tsarewa da kuma adanawa.
Ana iya tunawa cewa haɗin gwiwar tsakanin gwamnatin Jamus da hukumominta da NFC ya haifar da ƙaddamar da shirin digiri na gaba da digiri na farko na haɗin gwiwa tsakanin NFC/NFI-Unijos da Jami’ar Goethe a tsawon shekaru huɗu da suka gabata, wanda ya shafi al’adar bidiyo da ayyukan ajiyar tarihi.

