Gyaran rumbun lantarki na ƙasa ya kusa kammala – Hukumar TCN

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Kamfanin rarraba wutar lantarki na Nijeriya (TCN) ya bayyana cewa gyaran rumbun lantarki wanda ya faɗi a ranar Litinin yana ci gaba kuma ya kusan kammala.

A cikin wata sanarwa a ranar Talata, Manajan hulɗa da jama’a na TCN, Ndidi Mbah, ya bayyana cewa babban rumbun lantarki na ƙasa ya fuskanci matsala a ranar Litinin, 14 ga Oktoba, 2024 da misalin ƙarfe 6:48 na yamma.

“Sanarwar ta ce duk da cewa an fara dawo da tsarin wutar nan take, tare da tashar wutar lantarki ta Azura, an samu ci gaba wajen dawo da tsarin wutar da misalin ƙarfe 10:24 na safiyar yau, lokacin da aka fuskanci wani matsala da ta kawo cikas a aikin dawo da tsarin,” sanarwar ta bayyana.

“Duk da wannan cikas, Mbah ya ce TCN ta ci gaba da aikin dawo da rumbun, wanda ya kai matakin ci gaba, yana tabbatar da isar da wutar lantarki mai yawa zuwa kusan kashi 90% na tashoshin rarraba lantarki a faɗin ƙasar.”

Kamfanin ya bayyana cewa an dawo da wutar a yankin Abuja da sauran manyan cibiyoyin rarrabawa na ƙasa baki ɗaya.

A cewar Mbah, matsalar ba ta shafi tashar samar da iskar gas ta Ibom ba wacce aka keɓe daga rumbun lantarkin, tashar ibom ta ci gaba da ba da wuta ga yankuna a Kudu maso Kudu na ƙasar kamar Eket, Ekim, Uyo, da tashoshin wutar lantarki na 132kV a Itu yayin wannan lokaci.

By ukarofi