Ina samun jigon labarina a mafarki – Mrs Ibrahim 

Spread the love

“Rubutun batsa na bada gudunmawa a tsanar da ake wa marubuta”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Ba kowa ne zai iya gaya maka wacce ce Maryam Shu’aibu Sulaiman a cikin marubutan onlayin ba, amma da zarar ka ambaci sunan Mrs Ibrahim, sunan da aka fi saninta da shi, nan za ka sha labari iri-iri, game da ita. Ta kasance marubuciya mai halayen ƙwarai da sauƙin kai, mai son zumunci da kishin addini. Duk da kasancewar ba ta jima sosai a duniyar marubuta ba, amma tasirinta da sunanta ya karaɗe ko’ina. Littattafan da take rubutawa suna ɗauke da darussa masu muhimmanci game da rayuwa, inda take hannunka mai sanda ga masu aikata halayen da basu kamata ba, don su gyara. A tattaunawarta da wakilin Blueprint Manhaja, marubuciyar ta bayyana burinta na zama shahararriyar marubuciya da kowa ke sha’awar kwaikwayonta da yi mata addu’ar fatan alheri. Ga yadda hirar tasu ta kasance. A yi karatu lafiya. 

MANHAJA: Ki gabatar mana da kanki.

MANHAJA: Sunana Maryam Shu’aibu Sulaiman, amma a duniyar onlayin an fi sanina da Mrs Ibrahim. Ni marubuciyar littattafan Hausa ce a kafar yanar gizo wato onlayin, sannan kuma ni ƴar kasuwa ce, ina kuma aikin zane-zane a kwamfiyuta wato Graphics Design. 

Ki ba mu tarihin rayuwarki.

An haife ni ne a Jihar Yobe cikin ƙaramar Hukumar Potiskum. Na yi karatu tun daga matakin firamare har zuwa sakandire, duk a cikin garin Potiskum. Daga nan kuma ban samu na ci gaba da karatun ba, sai aka min aure, amma in sha Allah ina sa ran cigaba da karatun nan gaba. A ɓangaren karatun addini kuma, Alhamdulillah na sauke Alƙur’ani Mai Girma, ina kuma karatun littattafan addini, don inganta ibadata da rayuwa.

Ki bamu labarin yadda rayuwa ta kasance miki yayin tasowarki, wacce irin gwagwarmaya aka fuskanta?

To, dama ko wanne ɗan’adam da irin abinda ya ke fuskanta a rayuwarsa. Ni a gaskiya bai wuce akan maraicin da na tsinci kaina a ciki ba, kusan lokaci ɗaya na rasa iyayena, shi ne babban abinda na fuskanta a rayuwata, wanda ya zame min babban ƙalubale. Amma yanzu Alhamdulillah, komai ya zama daidai.

Wanne ƙalubale ki ka fuskanta da ya koya miki wani muhimmin darasi a rayuwarki?

ƙalubalen da na fuskanta bai wuce maraicin da na bayyana a baya ba. A lokacin da al’amarin ya faru na girgiza sosai, saboda ban taɓa kawowa a raina zan rasa iyayena a ƙanƙanin lokaci ba. Gaskiya maraici babban ciwo ne, wanda ba ya taɓa gogewa, sai dai raɗaɗin ya dinga raguwa kana samun sauƙi a hankali. Amma a duk lokacin da maraicin ya motsa ji kake tamkar a wannan lokacin ka rasa iyayenka. Na ɗauki darussa muhimmai, sai dai ba zan iya bayyanawa ba domin sirrina ne.

Wanne abu ne za ki iya cewa, ya taimaka wajen mayar da ke irin macen da yanzu kika zama?

Gaskiya bai wuce aure ba, domin shi ne ya mayar da ni duk abinda na zama a yanzu a rayuwa. 

Mene ne ya ja hankalinki kan rubutun adabi?

Abin da ya ba ni sha’awa har na fara rubutun littafin Hausa shi ne yadda nake karanta littattafan wasu marubutan. Wannan ya sa ina jin abin yana burgeni sosai, da kuma yadda suke faɗakarwa. Hasali ma a cikin karatun littattafan da nake yi na ƙaru da abubuwa da dama da suka taimaka min a rayuwata. 

A shekarun baya ban taɓa tunanin zan yi rubutu ba, kuma ban taso da tunanin yi ba, sai bayan da na yi aure ne sannan na fara tunanin haka. Kuma cikin yardar Allah, Allah Ya bani ikon farawa.

Yaushe kika fara tunanin fara rubuta labarin kanki, kuma ko za ki iya tuna yaya labarin yake?

A shekarar 2021 na fara tunanin fara rubutu. Kuma na fara ne da wani labari mai suna ‘Rayuwar Mariya’. Gaskiya naso labarin sosai, saboda wasu dalilai. 

Kawo yanzu kin rubuta littattafai guda nawa? Kawo sunayensu da bitar uku daga ciki.

Na rubuta littattafai kusan 7 zuwa 8. Akwai, ‘Rayuwar Mariya’, ‘Mugun Aboki’, ‘Uban Mijina Zan Aura’, ‘Maryama’, ‘Ƴar Gwani’, ‘Zaman Duniya’, ‘Cin Amanar Aure’, sai na takwas da nake kan yi yanzu wato ‘Rashin Sani’. 

Labarin ‘Rayuwar Mariya’, labarin ne na wata baiwar Allah wacce take rayuwarta cikin farinciki tare da mahafiyarta da kuma yayanta ɗaya tilo, wanda daga bisani suka rasa wannan mahaifiyartasu. Tun bayan rasuwarta, gabaɗayansu sun shiga wani hali, amma gaskiya yarinyar ta fi yayan shiga ɗimuwa wanda hakan ya janyo ta daina duk wani farin ciki a rayuwarta. Daga ƙarshe Allah Ya kawo mata mijin aure wanda ya yi sanadiyar canjawar rayuwarta ta dawo mace kamar kowa.

Shi kuma littafin ‘Mugun Aboki’, yana ɗauke ne da labarin wasu abokai guda uku wanda suke matuƙar son junansu, inda daga bisani ɗaya daga cikinsu ya ci amanarsu saboda abin duniya. Hakan kuma ya janyo har ya yi wa matar ɗaya abokin nasu fyaɗe. A ƙarshe kuma ya yi mummunar nadama tare da danasani wanda bai masa amfani ba.

Sannan kuma akwai littafin ‘Yar Gwani’, wanda ke ɗauke da labarin wata budurwa wadda ta fi ƙarfin iyayenta. Mahaifinta ya kasance babban malami, sai Allah Ya jarabceshi da wata fitinanniyar yarinya, wadda take yawon bin maza da kulob. Amma idan ka ganta kullum cikin hijabi, irin wanda ake yayi yanzu. Sai ka ga mace babu kayan arziƙi a jikinta, amma ta ɗora hijabi ta lulluɓe jikinta da shi. Kuma duk abinda take yi mahaifinta bai sani ba, sakamakon yadda mahaifiyar ke goya mata baya. A ƙarshe dai ta yi mummunar rayuwa da nadama sosai da sosai. 

Akwai kuma labarin ‘Zaman Duniya’, wanda labari ne na wata mata wacce ta yi matuƙar yarda da mijinta, amma kuma yake cin amanarta ba tare da ta sani ba. Kuma hakan ya samu ne saboda irin yadda take yi masa wajen nuna kulawa da soyayya, amma shi kuma sai yake cin amanarta tare da ƙanwarta, wacce suke ƴaƴan ‘yan’uwa. A ƙarshe dai su ma bata haifa musu ƴa mai ido ba, inda suka yi nadama sosai a rayuwar su.

Wanne littafin ne ya fara ɗaga sunanki a tsakanin marubuta?

Littafin ‘Ƴar Gwani’, shi ne ya sa aka ƙara sanina sosai a cikin marubuta. Saboda a lokacin da na fara littafin yabyi daidai da yayin wannan hijabin na Jalbab da ƴammata ke sanyawa. Shi ya sa ya samu karɓuwa har ni ma na yi suna a wajen jama’a, domin dama wasu abin yana ci musu tuwo a ƙwarya, ta dalilin haka kuwa na sake samun ƙwarin gwiwa sosai. 

Yaya alaƙarki da masu karatun littattafanki, ta yaya kike mu’amala da su?

Alhamdulillah, a gaskiya babu abinda zance da Allah sai godiya, domin akwai alaƙa mai ƙarfi tsakaninmu. Suna mutunta ni sosai, suna min sharhi akan labaraina da kuma bani shawarwari. 

Wanne abin farinciki ko akasin haka ne ya taɓa faruwa da ke ta sanadiyyar rubutu wanda ba za ki manta da su ba?

Abin farincikin dai shi ne irin yadda ake karɓar littattafaina da kuma yadda kullum nake samun masoya, hakan ba ƙaramin faranta min rai yake ba.

Ta yaya ki ke samun jigon da ki ke rubutu a kai?

Ina samun jigon labarina ne ta hanyar faruwar wani abu a zahiri, wani lokacin kuma a mafarki.

Wanne salon rubutu ne ya fi baki sha’awa, almara, yaƙe-yaƙe, sarauta, ko soyayya?

Gaskiya babu wanda ba na taɓawa, kodayake ban taɓa rubuta labarin da ya shafi yaƙe-yaƙe ba, sai dai ban sani ba ko nan gaba.

Wanne labari ne ya fi baki wahalar rubutawa ko ki ka fi jin sauƙin rubutunsa?

Labarin da ya fi bani wahalar rubutawa kawo yanzu shi ne, ‘Cin Amanar Aure’, wanda kuma ya ba ni sauƙin rubutawa shi ne, labarin ‘Zaman Duniya’. Gaskiya labarin bai ba ni wahala ba, kuma ban taɓa jin na ƙosa wajen rubuta wani labari kamarsa ba. 

Kin taɓa shiga wata gasar marubuta, kuma wanne sakamako ki ka samu?

Ina shiga gasar marubuta sosai, sai dai har yanzu Allah bai nufa na yi nasara ba. Amma hakan bai hana ni shiga wasu gasannin ba, domin a jikina nake jin zan kai ga nasara watarana, domin ko gasar Hikayata ta BBC Hausa ta bana na tura labarina, kuma ina fatan Allah Ya sa labarina ya yi zarra.

Wane ne ya fi taimaka miki wajen sanin ƙa’idojin rubutu, don inganta labarinki?

Akwai ƙungiyar da nake ciki, sannan akwai wani bawan Allah shi ma yake taimaka min da shawarwari sosai. 

Wacce ƙungiyar marubuta ki ke?

Ni mamba ce a ƙungiyar Royal Star Writers Association. Ita ce ƙungiyar da nake ciki kuma take bani gagarumar gudunmawa sosai, tun daga kan yadda zan kiyaye ƙa’idojin rubutu, har zuwa yadda zan tsara labarina a taƙaice. A gaskiya ina jin daɗin kasancewata a wannan ƙungiya, saboda yadda take taka muhimmiyar rawa wajen cigaban rubutuna.

Bani labarin gudunmawar da ki ka bayar a Zauren Marubuta na WhatsApp lokacin azumin watan Ramadan, inda ku ka gudanar da saukar karatun Alƙur’ani Mai Girma. Wacce rawa ki ka taka a lokacin?

E, gaskiya na bada gudunmawa sosai ta hanyar ba da himma da lokaci sosai a yayin karatun da aka yi. Sannan musamman nake kiran sauran ƴan’uwana idan basa onlayin, domin mu gabatar da karatun tare. Sannan kuma na bada gudunmawa wajen kiran mai gudanar da karatun ta hanyar kiran waya idan ya kasance ba ya kusa, ko kuma idan na lura lokacin karatun yana shirin wucewa. Gaskiya na ji daɗin karatun don ya yi matuƙar burgeni. Muna fatan Ubangiji Allah Ya nuna mana na bana lafiya. 

Wane ne madubin kwaikwayonki a cikin marubuta, maza ko mata?

Marubuciya Fauziyya D. Sulaiman ce wacce take matuƙar burge ni, game da rubuce-rubucenta da harkokinta na tallafawa mabuƙata. Ina karanta littattafanta sosai a baya. Ina ganin yadda take rubutu cikin tsari da salo mai kyau. Da kuma yadda take ƙoƙarin taimakawa mutane har ake mata kirari da Uwar Marayu. In sha Allahu nima idan na samu wata dama, kuma Allah Ya hore min nima zan fara kwaikwayonta, ta hanyar taimakawa mutane.

Wanne abu ne kike ganin idan kin samu dama za ki iya yi don kawo canji a harkar rubutun adabi?

Babu abin da yake tsaya min a rai kamar in ga na kawo ƙarshen rubutun batsa a duniyar marubuta, domin tsare mutuncin martabar marubuta. Babu shakka rubutun batsa yana bada gudunmawa gagaruma wajen tsanar da wasu daga cikin mutane suke yi wa marubuta, musamman na onlayin. Gani suke yi kamar duka haka halin mu ɗaya ne. Alhalin marubutan batsan ko kaso 20 ba su kai ba a cikin marubuta.

Mene ne babban burinki nan gaba a harkar rubutu?

Babban burina shi ne na zama shahararriyar mubuciya a duniyar marubuta, ta yadda a duk lokacin da ambaci sunan marubuta, sai an sako sunan Mrs Ibrahim. Ina son sunana ya zama daga cikin waɗanda manazarta da masu sharhi da marubuta bakiɗaya za su yabawa, saboda gudunmawar da nake bayarwa. Ina son in zama abar kwaikwayon marubuta ƴan baya, ko da bayan raina.

Wanne karin magana ne ke tasiri a rayuwarki?

Shine mahaƙurci mawadaci.

Na gode da samun lokaci da ki ka tattauna da mu.

Ni ma ina godiya.

By ukarofi