Gwamna Nasir ya ƙaddamar da aikin tagwayen hanyoyi mai tsawon kilomita 6.4 kan biliyan N7.23 a Argungu

Spread the love

Daga JAMEEL GULMA a Kebbi 

Gwamnan Jihar Kebbi Malam Nasir Idris ya ƙaddamar da aikin tagwayen hanyoyi mai tsawon kimanin kilomita  6.4 a kan titin tsohuwar Bypass dake garin Argungu.

Da yake jawabi a wurin taron ƙaddamar da aikin ranar Talatar da ta gabata, Maigirma Gwamna Malam Nasir Idris ya bayyana cewa wannan yana ɗaya daga cikin alƙawurran da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe da kuma wani ƙoƙari da wannan gwamnati take yi wajen raya ƙauyuka da birane a faɗin jihar.

Ya bayyana cewa aikin hanyar ya haɗa da gina magudanun ruwa da kuma kwalbatoci da kuma sanya fitilun titi masu aiki da hasken rana.

Yanzu haka dai an bai wa Amirco Uniɓersal Concept Ltd kashi arba’in a matsayin somintabi don ganin sun yi aiki mai inganci da kuma kammala shi a cikin lokacin da aka yi sharaɗi.

Ya bayar da tabbacin gwamnati za ta sanya ido sosai wajen tabbatar da an yi aiki mai inganci saboda ba za mu bayarda aiki ba kuma mu koma ofis ko gida mu zauna ba, za mu cigaba bibiyar aikin har sai an kammala shi in Sha Allahu.

Ya kuma yi wa al’ummar Argungu da kewaye albishir da cewa in Sha Allahu nan da sati mai zuwa za a soma aikin gyaran babbar asibitin dake Argungu bisa ga la’akari da yanayin ta ya kasance yanzu.

Shugaban kamfanin Amirco Uniɓersal Concept Ltd Dakta Hassan Mahadi ya yaba wa gwamnan Kebbi musamman saboda amfani da kamfunan cikin gida wanda ya ce ba shakka ya nuna yana da kishin ƙasarsa. 

Ya bayar da tabbacin kamfanin zai gudanar da aiki mai inganci kamar yadda aka buƙata inda ya ce za su kammala aikin cikin watanni shida kafin wata goma sha biyu da aka yi sharaɗi.

Maimartaba Sarkin Kabin Argungu, Alhaji Sama’ila Muhammad Mera ya yaba wa Maigirma Gwamna bisa gudanar da wannan aikin a Masarautar Argungu.

Basaraken ya zayyano waɗansu daga cikin ayyukan ci gaba da Gwamna Nasir ya gudanar a masarautar Argungu ciki har da ɓangaren ilmi da kuma irin taimakon da aka bai wa al’ummar da ambaliyar ruwa ya raba da muhallansu a jihar Kebbi.

Ya kuma yi kira ga al’ummar da wannan aikin da su bai wa ma’aikatan kamfanin haɗin kai don ganin an samu kammala aikin cikin nasara.

By ukarofi