NPFL: Rivers United ta sake hawa saman tebur

Spread the love

Rivers United sun ci gaba da samun nasara s a gasar Firimiyan Ƙwallon Ƙafa ta Nijeriya (NPFL) bayan sun doke Shooting Stars da ci 2-0 a Fatakwal, yayin da waɗanda ke saman teburin gasar Remo Stars suka sha kashi hannun Plateau United da ci 3-1 a Jos.

Rivers United, ƙarƙashin jagorancin tsohon kocin Super Eagles Finidi George, yanzu suna da maki 17 daga wasa bakwai, yayin da Remo Stars suka sauka daga matsayi na farko tare da maki 15.

Rivers United sun jira zuwa rabin lokaci na biyu kafin su zura ƙwallo ta hannun Aniekeme Okon a minti na 51.

Ndifreke Effiong ya shigo daga benci ya tabbatar da nasarar a minti na 65.

Shooting Stars sun koma su 10 bayan Alex Aghahowa ya samu jan kati jim kaɗan bayan an ci ƙwallon farko.

Bayelsa United yanzu suna cikin haɗarin faɗuwa cikin yankin sauka daga gasar bayan sun sha kashi da ci 3-0 a hannun Bendel Insurance a Benin.

Katsina United sun doke Akwa United da ci 1-0, yayin da Heartland FC da Ikorodu City waɗanda ke gwagwarmaya don kauce wa sauka daga gasar suka tashi 1-1 a Owerri.

Ikorodu sun buga minti 10 na ƙarshe da ƙarancin ɗan wasa bayan Toyeeb Aiyigbe ya samu katin gargadi na biyu.

By ukarofi