Sojoji sun kashe ƴan ta’adda huɗu da ƙwato makamai

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A yayin wasu atisaye da jami’an sojojin Nijeriya suka gudanar, sun yi nasarar kama wata mata mai safarar makamai da kuma tarwatsa ƴan ta’adda inda suka ƙwato muggan makamai.

A lokacin da suka kai farmaki, jami’an sun kuma yi nasarar kashe wasu manyan ƴan ta’adda tare da kama wasu sanannu daga cikin su.

A ranar 17 ga watan Oktoba ne jami’an suka kama wata mata da takwarata a tashar mota ta Barikin Ladi da ke Jihar Filato da laifin safarar makamai ga ƴan ta’adda a Jihar Zamfara.

Hakan ya sa jami’an suka yi nasarar kama wani mai suna Alhaji Adamu Bahar wanda ya na ɗaya daga cikin waɗanda ake nema ruwa a jallo tare da gano wasu muggan makamai a gidansa.

A wani labarin kuma, sojoji sun yi nasarar kashe wasu mayaƙan Boko Haram guda biyu da ƙwato makamai da dama a lokacin da su ke karɓar harajin da suka ƙaƙaba wa al’umma a ƙauyen Ngazargamu da ke ƙaramar hukumar Gujba a Jihar Yobe.

Kamar haka jami’an soji suka kashe wasu ƴan ta’addar ISWAP guda biyu da ƙwato makamai da wasu ababe a Jihar Borno.

By Babaji