Ci gaba daga makon jiya
Illarsa ga fata da gashi
Yawan aikata istimna’i na da illa ga fata da kuma gashi. A lokacin saduwa, namiji da mace dukkansu su na fitar da ruwa da yake mai santsi, domin rage jin zafi gogayya (friction) tsakanin fatar zakarin namiji da fatar farjin mace; shi kuwa auren hannu ba shi da wannan. Mutum ɗaya ne kaɗai ke wasa da gabansa ko gabanta.
Duk da cewa ko mutum ɗaya ne akwai ruwa da ya ke fita, ko kuma wasu za su ce ai su na shafa mai, domin cimma sauƙin wannan gogayya tsakanin hannunsu da gabansu, to tsuguno ba ta ƙare ba, tun da an keta yadda Sarkin halitta ya tsara.
Wannan yawan guga da ake yi wa kafar farji ko azzakari zai iya sanya fatar wajen ta siɗe, ta yi ja ko ta dinga ƙaiƙayi ko ta yi ƙuraje; ya danganta da yawan aikata abin, wato sau nawa mutum ya ke yi a rana ko a sati.
Haka kuma idan mace na amfani da kowanne irin mai wajen cimma wannan manufa, cuɗanyar man da halittun da ke matucinta kan iya jawo sabuwar matsala.
Misali; wani nazarin masana a ƙasar Ghana ya nuna cewa, mata masu yin istimna’i da zakarin roba suna cikin haɗari, saboda sinadarin da aka haɗa shi abun kemikal ne mai suna ‘phthalatic acid’. Yawan amfani da shi zai iya haifar da matsala.
Haka kuma yawan yin istimna’i ya na da alaƙa da zubewar gashi, saboda akwai wani sinadari a jikin mutum wanda ake tsarto shi da yawa cikin jini. Idan ya yi yawa a cikin jini sai ya kurɗa ya tafi inda jijiyoyin gashi su ke ya ɗamfare da su. Ta haka zai hana gashi miƙewa da girma, wanda a ƙarshe gashin zai karye. Faruwar hakan a jijiyoyin gashi da yawa shi ke kawo zubewar gashi.
Idan haka ya faru a kan mutum, zai iya jawo ma sa sanƙo!
A mata ma su yi, su kan fuskanci zubewar gashin kai, na hammata ko na gaba. Maza kuma ya kan jawo musu zubewa ko karyewar gemu ko ƙasumba. Amma jiki iri-iri ne, jikinmu ya bambanta, kamar yadda fuskokinmu suka bambanta.
Naku; MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI, ©MIAbdullahi 2024
