Kuɗaɗen ƙananan hukumomi: Gwamnoni da ciyamomi sun ƙulla yarjejeniyar sirri

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A yayin da ake ci gaba da samun ƙarin haske, rahotanni sun ce wasu gwamnonin Nijeriya sun ƙulla yarjejeniyar sirri da shugabannin ƙananan hukumomi domin ci gaba da kula da kuɗaɗen ƙananan hukumomi, duk kuwa da hukuncin da Kotun ƙoli ta yanke na bai wa ƙananan hukumomi 774 ’yancin cin gashin kansu.

A cewar majiyoyi, waɗannan yarjejeniyoyin sun haɗa da alƙawurran biyayya da yarjejeniyar ɓoye da nufin kaucewa umarnin raba kuɗaɗe kai tsaye ga ƙananan hukumomin.

Hukuncin da Kotun ƙoli ta yanke a ranar 11 ga watan Yuli ya tilasta biyan kuɗaɗe kai tsaye daga asusun tarayya zuwa ƙananan hukumomi, wanda ke nuna gagarumin sauyi a tsarin hada-hadar kuɗj na tarayyar Nijeriya.

Bayan wannan hukunci, gwamnatin tarayya a ranar 20 ga watan Agusta, ta kafa kwamitin ma’aikatu mai mutane 10, ƙarƙashin jagorancin sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, domin tabbatar da aiwatar da hukuncin.

Ana sa ran kwamitin zai miƙa rahotonsa a ranar 14 ga watan Oktoba.

Sai dai jim kaɗan bayan yanke hukuncin, gwamnonin jihohin sun buƙaci a ɗage zaɓe na tsawon watanni uku a shirin rabon kuɗacen kai tsaye domin ba su damar gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi.

Tun a wancan lokaci jihohin da suka haɗa da Ebonyi, Bauchi, Kebbi, Oyo, Kwara, Imo, Enugu, Sokoto, Akwa Ibom, Anambra, Benuwai da Ribas suka gudanar da zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi.

Duk da yadda ake sa ran samun yancin cin gashin kai, sakamakon binciken da jaridar Sunday Punch ta yi ya nuna cewa gwamnonin na ci gaba da rara-gefen riƙe madafun iko da kuɗaɗen ciyamomi ta hanyar ƙulla yarjejeniya a asirce.

By ukarofi