Shugaba Tinubu ya rushe ma’aikatu biyu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnatin Tarayyata rushe Ma’aikatun kula da yankin Nija-Delta da na Ci-gaban Wasanni.

Hakan na zuwa ne yayin wani zama da Majalisar Zartarwa, FEC ta yi a ranar Laraba, a Abuja.

Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya wallafa batun a shafinsa na X.

Za a samar da Ma’aikatar Ci-gaban Shiyya don kula da lamurran da suka shafi shiyyoyin ƙasar ciki har da hukumomin ci-gaban Nija-Delta, ci-gaban Arewa-maso-Yammaci, Kudu-maso-Yammaci da kuma Arewa-maso-Gabas.

Hukumar Kula da Wasanni ta Ƙasa za ta ɗauki ragamar ayyukan Ma’aikatar Wasanni.

Majalisar Zartarwar ta kuma haɗe Ma’aikatar Walwala da Jin-daɗi da Ma’aikatar Al’adu.

Saidai, Mista Onanuga bai bayyana makomar ministocin ma’aikatun da aka rushe ba.

By Babaji