Nijeriya za ta ranto dala miliyan 600 don sayo jiragen yaƙi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Nijeriya ta amince da karɓo rancen sama da dala miliyan 600 domin sayen wasu jiragen yaƙi samfurin Italiya M-346.

Gwamnatin na fatan samun jiragen ga rundunar sojin sama domin kai hare-hare a farkon shekarar 2025.

Nijeriya dai ta ƙara yawan kuɗaɗen da take kashewa a fannin soji yayin da take yaƙi da ‘yan bindiga tsawon shekaru musamman a arewacin ƙasar.

Group Kaftin Saddiƙ Shehu wani masanin tsaro a Nijeriya, ya ce duk da wannan yunƙuri na gwamnati na sayen waɗannan jirage, har yanzu sojojin ƙasar na buƙatar ƙarin kayan aiki.

Haka kuma masanin ya ce, babbar mastalar da kayan aikin sojin ƙasar ke fuskanta ita ce matsalar rashin iya gyara su, musamman jirgin saman, wanda idan ya samu wata matsala ba a iya gyara su a nan, wanda haka ke tilasta wa gwamnati sayo wani sabo, maimakon a gyara wanda ake da su.

‘‘Duk da maganar da ake yi sojojinmu ba su da isassun kayan aiki, wasu kayan aikin sun tsufa wasu kuma gyaransu ne mastalar, wanda ka ga mu ba mu yi nisa ba a fannin gyaransu, wanda daga ƙarshe dole a je a sayo sabo,” inji Group Kaftin Saddiƙ.

Haka kuma ya ce sayo jirgin zai bayar da gudunmawa wajen magance ayyukan Boko Haram da ‘yan fashin daji.

A cewarsa, “wannan jirgi, ana iya amfani da shi wajen harbo abu daga sama zuwa ƙasa, sannan za a iya amfani da shi wajen bayar da horo ga waɗanda za su tuƙa jirgin,” inji shi.

An dai fara batun sayen waɗannan jiragen yaƙi ne lokacin mulkin gwamantin da ta gabata ta Muhammad Buhari, kwastam sai kuma aka ji gwamantin Bola Ahmed Tinubu ta sanar da amincewa da ciyo bashin kuɗi don siyo waɗannan jirage.

Group Kaftin Saddiƙ Shehu ya ce ‘shi siyen makami ba abu ne na yanzu-yanzu ba, sai an bi wasu matakai sannan a tsayar da magana.

Haka kuma ya yi jan hakalin cewar kayan aikin soja na da matuƙar tsada, wanda kasafin kuɗin shekara-shekara ake gabatar da su, yawancin kasafin na shekara ba zai yiwu sojoji su iya siyo kayan aikin da suke buƙata da shi ba.

Sai dai Kaftin Saddiƙ Shehu ɗin ya ce, rashin bincike na daga cikin abubuwan da ke sanyawa a wasu lokuta sayen irin waɗannan jirage masu tsada kan zame mata ƙadangaren bakin tulu, saboda rashin kyakkyawan bincike, da ke sanyawa sayen jiragen zame wa Nijeriya alaƙaƙai.

“Ka ga akwai wasu jirage da Shugaba Buhari ya bayar aka siyo daga Pakistan F17 guda 24 amma a yanzu babu ko da guda ɗaya da yake aiki, wanda ka ga kenan akwai ƙamshin gaskiya kan sayensu kan zama alaƙaƙai,” a cewar Group Kaftin Saddiƙ Shehu.

By ukarofi