‘Yan bindiga sun kashe ɗan takarar shugaban ƙasa

Spread the love

An harbe lauya babba ɗan takarar adawa a Mozambiƙue Venancio Mondlane, wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen ranar 9 ga Oktoba a Maputo a ranar Asabar.

An kashe lauyan, Elvino Dias, tare da wani ɗan takara, Paulo Guambe, daga Jam’iyyar Podemos da ke goyon bayan Mondlane.

Wasu ‘yan bindiga biyu ne suka harbe motarsu yayin da motar take tsaye a kan hanyar da ke tsakiyar babban birnin ƙasar, kamar yadda shaidu suka bayyana.

Shugaban Podemos Albino Forƙuilha ne ya tabbatarwa kamfanin dilancin labaren AFP kisan gillar, yayin da ƙungiyar lauyoyin ƙasar ta nuna matuƙar kaɗuwarta da mutuwar Dias.

Wata ƙungiyar masu sa ido kan ƙungiyoyin farar hula, Mais Integridade, ta kira kisan marasa rai da “aiki na tsoratarwa” da ke barazana ga mulkin dimokraɗiyya.

‘Yan sandan sun ce an fara bincike amma ba a kai ga tabbatar da sunayen mutanen biyu da aka kashe ba.

ƙungiyar Tarayyar Turai ta fitar da wata sanarwa inda ta yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa Dias da Guambe tare da yin kira da a gudanar da cikakken bincike na gaskiya “wanda zai gurfanar da waɗanda ke da hannu a wannan mummunar aika-aika.”

“A tsarin dimokuraɗiyya, babu gurbin kashe-kashen da suka shafi siyasa,” inji shi.

Mozambik dai na dakon sakamakon zaɓen a hukumance a faɗin ƙasar. Ana sa ran za a fara sanar da sakamakon ne a ranar 24 ga Oktoba.

Mondlane, wanda ya ƙalubalanci Jam’iyyar Frelimo da ke mulkin Mozambiƙue tun bayan samun ‘yancin kai shekaru 49 da suka gabata, ya yi iƙirarin samun nasara tun a kashe garin ranar zaɓe.

Kuma ya yi zargin tafka maguɗin zaɓe, biyo bayan yadda Frelimo ke iƙirarin shi ne kan gaba a ƙidayar ƙuri’un, kuma ya yi kira da a gudanar da zanga-zanga a ranar Litinin.

By ukarofi