Ya gano maɗaurin aurensa ne mahaifin ’ya’yansa

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wani mutum ya shiga cikin ɗimuwa bayan ya gano cewa fasto da ya ɗaura aurensa, shi ne mahaifin ’ya’yansa biyu.

Wani labari mai ban mamaki, wanda ya faru a Zimbabwe, ya bayyana yadda aka umarci wani fasto daga cocin End Time Messages a Chiredzi, da ya ɗauri nauyin wasu yara.

Binciken DNA ya nuna cewa, Fasto ɓhetu shi ne mahaifin ’ya’ya biyu da Eunice Mururi ta haifa bayan aurensu da Farai Hatirarami.

Bayan gaskiya ta bayyana, auren Mururi da Hatirarami ya rushe. Yanzu haka dai Mururi ya maka Fasto ɓhetu ƙara kotu, inda yake neman fastom su riƙa ba da dala dala 700 duk wata ga yaransu masu shekaru 8 da 4.

Fasto ɓhetu ya shigar da ƙara mai ban mamaki a gaban kotu, inda ya amince da cewa shi ne mahaifin yara biyu tare da wata mata da ya ɗaura mata aure. Duk da haka, yanzu yana neman a rage kuɗin kula da yaran, inda ya ce samun kuɗinsa na yau da kullum ba zai iya akwatar da hakan ba.

Lauyansa, Farai Chauke, ya bayar da hujjar cewa ɓhetu ba shi da albashi mai tsoka, wanda ya iyakance abin da fastom zai iya biya da ZiG 150 kan kowane yaro. Shari’ar ɗaukar nauyin yaran Fasto ɓhetu ta bar al’umma cikin firgici.

By ukarofi