Boko Haram za ta iya amfani da yaran da ba sa zuwa makaranta – Obasanjo

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Tsohon shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya ce ƙaruwar yaran da ba sa zuwa makaranta a ƙasar, na da matuƙar haɗari ga al’ummar ƙasar nan gaba.

Ya ce, sama da yara miliyan 20 da ba sa zuwa makaranta a Nijeriya za su iya tsunduma cikin ayyuka Boko Haram da ’yan bindiga cikin shekaru 10 zuwa 15 masu zuwa.

Tsohon shugaban ƙasar ya bayyana haka ne a Bauchi ranar Lahadi a wurin bikin Aaddamar da wasu zaɓaɓɓun ayyuka da Gwamna Bala Mohammed ya aiwatar.

“Bankin Duniya ya ce muna da yara sama da miliyan 20 da ya kamata su kasance a makaranta waɗanda ba sa zuwa makaranta ga al’ummar kusan miliyan 230.

“Don haka, kashi 10 cikin 100 na al’ummarmu da ya kamata su kasance a makaranta da ba sa makaranta. Gwamna, Sarakunanka, ’yan uwa, a yi hattara domin kuwa ’yan Boko Haram na iya ɗaukar waɗannan yara a nan gaba, babu wanda ya isa ya dakatar da hakan,” inji Obasanjo.

Ya ce rashin ba yaran kayan aikin da za su bunƙasa iyawa da ƙarfin su ya sa ‘yan Boko Haram da ‘yan fashi suke amfani da su.

By ukarofi